Jonathan Na Kokarin Hana Bincike Akan Minostocin Shi Da Masu Bashi Shawara
Rahotanni sun nuna cewa kokarin karshe da shugaba Jonathan yake yi don hana binciken tsohonnin Ministocin shi da mataimakan shi daga Shugaba Buhari ya fadi.
Shugaba Jonathan wanda ya dogara da Janar Abdussalami wanda ya shugabanci Kwamitin zaman lafiya na hannun ta mulki ne ke mai kokarin.
Jaridar The Nation tace Janar Abdusalami ya samu ganawa da Buhari akan bukatar ta Jonathan. Shugaba Jonathan na bukatar su hadu da Shugaba Buhari tare da Janar Abdulsalami, amma kokarin Janar Abdulsalami bai cinma ruwa ba saboda aiyukan Shugaban Kasa bayan da janar Abdussalami ya kokarta wajen ganin shugaban Kasa sau Biyar.
Jonathan wanda ya dawo Najeriya satin daya wuce ya damu akan yanayin da tsohon mai bashi shawar akan tsaro (NSA), Kanar Sambo Dasuki mai murabus da kuma tsohon shugaban Jam’an tsaron shi (CSO) Gordon Obua suke cike.
An tabbatar a jiya cewa tsohon Dan sandan dake tsayawa bayan tsohon Shugaban kasa (ADC) wanda daga baya ya zama mai kula da tsaron tsohon shugaban kasan kasan Mista Moses Jitoboh an kama shi.
Akwai jita-jita cewa kama Mista Jitoboh da akayi yana da alaka da hukumar hana cin hanci da rashawa (EFCC), amma wani Jami’i a hukumar ya karyata hakan. Da yawa daga cikin Ministocin Jonathan sun koma Kasashen Waje bayan da aka hannun ta mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
The post Jonathan Na Kokarin Hana Bincike Akan Minostocin Shi Da Masu Bashi Shawara appeared first on News on Naij.com | Today's Nigeria Breaking news & headlines..
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us