Sports Betting

Trending

random

Ko Kun San: Sabbin Shuwagabannin Gudanarwa Na Majalisar Wakilai

A yanzu ba labari bane cewa ana rikici a cikin majalisar wakilai. Abunda jama’a basu sani ba shine su wanen sabbin shuwagabannin karamar majalisar.

Naij.com tayi bincike akan sabbin shuwagabannin wadanda zasu ja ragamar majalisar nan da shekara 4 masu zuwa.

1. Honarabul Femi Gbajabiamila: shugaban majalisa.

Wasu da yawa sunce zaben shi da akayi yayi daidai. Shi kwararren danmajalisa ne. Shine tsohun shugaban marasa rinjaye na tsohuwar majalisa ta 7. Shi ke wakiltar Surulere 1. Dogara ne ya kada shi a zaben kakakin majalisa da akayi. Amma Gbajabiamila baiyi wata-wata yayi mashi murna. Amma wasu na zargin cewa shine ke hura wuta saboda yaki ya yarda da shugabancin mataimakin Dogara.

2. Buba Jibrin: Mataimakin shugaban majalisa.

Jibrin dai ya kasance a majalisa tun 2011. Yana wakiltar jihar Kogi ne. Shine mai magana da yawun kungiyar dake goyan baya Dogara mai suna Consolidated group. Jibrin ya ksance mai magana sosai musamman lokacin da ake rikicin majalisar. Kuma dama tun farko shine Dogara yaso yaba mukamin mataimakin shugaban majalisar tun farkon lokacin da ya fiddo da jarin sunayen wadanda yake so ya ba mukami. Amma a lokacin babu Gbajabiamila.

3.  Honarabul Ado Doguwa: Shugaban masu tsawatarwa.

Shine wakilin mazabun Tudun Wada/ Dogawa. Yana da ilimi akan harkokin majalisa. Ya samu gama karatun sa da first class a kan karatun Jarida a jami’ar Bayero dake Kano. Ya taba zaman shugaban zauren yan majalisoshin Afirika na cinma muradin karni. Yana cikin masu goyon bayan Gbajabiamila. Shine wanda Dogara yaso yaba shugaban majalisa kafin ayi zaman sulhu tsakaninsu da shugaba Buhari.

4. Honarabul Paul Iriase: mataimakin shugaba mai tsawatarwa.

Shi tsohon Sakataren gwamnatin jihar Edo ne. Yana da masters akan karatun Akawuntanci. Kuma shi mamba ne na institute of management da kuma charted accountants of Nigeria. Shike wakiltar mazabar Owan dake Edo. Dan Jam’iyyar APC ne. kuma da yaso ya nemi mukamin kakakin majalisa kafin ya hakura yayi biyyaya ga jam’iyya ya goyi bayan Gbajabiamila.

Dogara dai an zabe shi kakakin majalisa duk da cewa jam’iyyar shi ba haka taso ba. Ya samu kuri’u 182, amma shi Gbajabiamilabya samu 174.

Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.

The post Ko Kun San: Sabbin Shuwagabannin Gudanarwa Na Majalisar Wakilai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


Ko Kun San: Sabbin Shuwagabannin Gudanarwa Na Majalisar Wakilai Reviewed by Olusola Bodunde on 07:14 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.