Babbar Sallah: APC, Atiku Sun Gaishe Da Yan Najeriya
Jam’iyyar APC nayi ma daukacin musulman Najeriya murnar zuwan babbar sallah. Sannan kuma sana fatan za’ayi sallah cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Lai Mohammed
Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana wanna a ranar Laraba 23, ga watan Satumba inda yayi godiya ga yan Najeriya akan jajircewar su wajen samun canji. Jaridar Vanguard ta ruwaito.
Yace: “Kasancewar wanna Sallah ta farko wanda za’ayi tun samun canji, muna godiya ga yan Najeriya akan gudunmuwar da suka bada. A hankali zamuyi gyara saboda an dade ana barna a mulkin daya wuce.
Jam’iyyar tayi addua Allah ya amshi duka ibadun yan Najeriya kuma najeriya ta cigaba da bunkasa. Haka zalika shima tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bayyana haka a shafin shi na Twitter inda ya bukaci kowa da dan Najeriya ya zama wakilin addin shi na gari.
Yace: “Musulmai suyi magana da murya daya akan ta’addanci domin yana bata ma addinin dama su bin shi suna. Fa’idojin Babbar Sallah suna da dama kuma kada a bari su tafi da bikin sannan kuma kada a manta su bayan bikin ya wuce.”
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.
The post Babbar Sallah: APC, Atiku Sun Gaishe Da Yan Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
Babbar Sallah: APC, Atiku Sun Gaishe Da Yan Najeriya
Reviewed by Olusola Bodunde
on
10:42
Rating:
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us