Fadar shugaban kasa ta yaba ma majalisar Najeriya
– Fadar shugaban kasa ta yaba ma sanatoci akan amincewa da kasafin kudi na 2016
– Kasafin kudin kimanin watanni 3 ke nana ana tanatance shi
Shugaban kasa Buhari a gaban majalisa lokacin da ya gabatar da kasafin kudin
amincewa da kasafin kudi na 2016 da yan majalisa sukayi ya samu yabo daga fadar shugaban kasa.
KU KARANTA: Hukumar DSS ta saki wani dan majalisar Jihar Ekiti data tsare
Inda yake ganawa da yan jarida, Ita Enang, mai taimaka ma shugaban kasa akan sha’anin majalisar dattawa, ya yaba ba duka sanatocin akan kokarin da sukayi akan kasafin kudi na 2016.
Yace ” Nabi duka yadda abubuwan ke tafiya kuma naga yadda sanatocin suka nunakwarewa wajen ganin an amince da kasafin kudin, musaam shugabanin kwamiti daban daban da yan kwamitocin.
Sannan kuma ya yaba ma sanatocin akan suka amince da MTEF da FSP wanda dashi ne aka amince da kasafin kudin.
Idan za’a iya tunawa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai kasafin kudin a ranar 22 ga watan Disamba. Amma daga baya an samu rudani wanda hakan ya sanya aka yima kasafin kudin gyare gayare.
Daga baya ne bayan da aka duba sai aka fara zama kan kasafin kudin in kwamitoci suka duba nasu sannan a jiya aka amince da kasafin kudin na 2016.
The post Fadar shugaban kasa ta yaba ma majalisar Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us