Sports Betting

Trending

random

Kungiyar IPOB na zargin DSS da yunkurin kashe Nnamdi Kanu

– Kungiyar IPOB na zargin gwamnatin Tarayya da hukumar DSS akan yunkurin kashe nnamdi Kanu idan aka sake zama Kotu.

– Kungiyar ta bayyana cewa wasu gwamnonin yankin Kudu maso Gabas ne suka hada shirin

Nnamdi Kanu

Daraktan Rediyon Biafra, Nnamdi Kanu

Kungiyar IPOB na zargin gwamnatin tarayya, hukumar DSS, wasu gwamnoni guda 3 daga yankin Kudu maso Gabasa, mambobin majalisar Najeriya da yunkurin kashe shugaban kungiyar kuma Daraktan Rediyon Biafra.

KU KARANTA: 

A cewar kungiyar, yunkurin zaya auku ne akan hanyar kai Nnamdi Kanu kotu a cigaba da shari’ar da akeyi mashi. Wanna sakon ya fito ne daga jami’a mai hudda da jama’a ta kungiyar, Emma Powerful, jaridar Vangurad ta ruwaito.

Tace ” Taron ya gudana ne a gaban wasu manyan yan APC, gwamnoni guda 3 daga yankin kudu maso Gabas, sanatoci daga yankin da kuma makiyan kafa kasar mu ta Biafra.

” Abunda suka shirya shine a bude ma motar da yake ciki wuta akan hanyar shi zuwa kotu inda a haka ne zasu kashe shi.

A wani labarin kuma kungiyar MASSOB ta kai koken ta ga majalisar dinkin duniya inda ta zargi gwamnatin Najeriya da kake mambobin ta a lokacin da suke gudanar da zanga-zanga ta lumana.

Idan za’a iya tunawa. Nnamdi Kanu ya share kimanin watannin 9 ke nan a tsare tun lokacin da aka kama shi a shekarar data wuce. Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin hukunta shi akan laifin juyin gwamnati.

The post Kungiyar IPOB na zargin DSS da yunkurin kashe Nnamdi Kanu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


Kungiyar IPOB na zargin DSS da yunkurin kashe Nnamdi Kanu Reviewed by Olusola Bodunde on 00:28 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.