Matasa na neman Buhari ya basu N5000
– Matasa sun nemi Buhari ya basu N5000 din da yayi masu alkawari
– Shugaban kasa yayi alkawarin ba matasa N5000 idan ya hau mulki
– Ya bayyana cewa bazaya iya bada N5000 a makon daya wuce
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Yan siyasa da masu kula da lamurran kasa na jira suga yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari zaya cika alkawarin ba matasa N5000 da yayi lokacin yakin neman zabe.
KU KARANTA: Buhari ya nada Mrs Adejoke mai bashi shawara
A lokacin yakin neman zabe, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin ba matasa marar aikin yi N5000 a kowanne wata domin ya rage masu radadin rashin kudi.
Amma daga baya da shugaban kasa ya hau mulki, a makon daya wuce a kasar Saudiyya, shugaban kasa ya bayyana cewa ba zaya iya ba matasa N5000 din yayi alkawari ba. Ya bayyana cewa kara ya gina makarantu da sauran abubuwan da duka al’umma zasu amfana dasu.
KU KLARANTA: Buhari ya canza ma’aikata 184
Sakamakon fadin haka da yayi ya jawo mashi Allah wadai daga bakin matasa da yawa. Wani matsa mai suna Tony a karkashin kungiyar matasan da suka gama makaranta basu da aikin yi, yayi Allah wadai da matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka inda yace ” Daman gwamnati bada da sahihanci, kuma bata cikin alkawarin ta.”
The post Matasa na neman Buhari ya basu N5000 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us