Mun kama kwamandan Boko Haram – Soji
– Naij.com ta samu hotunan wani kwamandan Boko Haram da sojojin Najeriya suka kama
– An kubutar da wata yarinya yar shekara 3 daga hannun shi
Kwamandan Boko Haram da sojojin Najeriya suka kama
A wani farmaki da aka kaima kungiyar Boko Haram a jiya, sojojin Najeriya sun kubutar da wata yarinya yar shekara 3 daga hannun shi inda shi kuma aka kama shi. Wannan sakon ya fito ne daga kanar Sani Usman Kakasheka wanda shine jami’i mai hudda da jama’a na hukumar sojin kasa.
KU KARANTA: Yan Boko Haram sun farma garin Bita
Yarinyar da aka Kubutar
Yace ” Zaratan spojojin jin mun na Bataliya ta 7 sun farma wasu yan Boko Haram dake kam mashin guda 3 akan hanyar Kokeno wadda ta hada Dabam Masar inda suka kama wani kwamandan su
Bindigogin yan Boko Haram da aka amshe
KU KARANTA: An kama Yan Boko Haram 3 a Kamaru
“Cikin abubuwan da aka amshe daga hannun su ya hada da;bindiga kirar AK-47 guda 3, mashin guda 2, Wayar Salula guda 4, kayan abinci da sauran su.
Mashinan da aka amshe daga hannun su
Ya kuma bayyana cewa sojojin Najeriya na Task Force na 118 sunyi arangama da Yan Boko Haram a garin Ma’ala inda suka kashe daya kuma suka kama daya. An samu bindiga kirar AK-47 guda da tulin harsashi da sauran wasu abubuwa.
Wayoyin salulr yan Boko Haram da aka amshe
The post Mun kama kwamandan Boko Haram – Soji appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us