Sojojin Najeriya sun fatattaki yan Boko Haram a Jere
– Sojojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram a Dipcheri, Jere da Cholgo
– Sojojin sun amshe motoci, makamai da abubuwa daga hannun su.
Wani sansani yan Boko Haram da ake konawa
Sojin Najeriya bayan da suka hallaka yan Boko Haram suna zagaye
Bayan nasarar da aka samu daga sojojin runduna ta Task Force ta 151, 21 Brigade, sojojin Task Force na 155, Brigade ta 21 sun hallaka yan Boko Haram a Dipcheri, Jere da kuma a Chogolo.
Sojin Najeriya rike da tutar yan kingiyar Boko Haram
Jami’i mai hudda da jama’a na sojin kasa na Najeriya, Kanar Sani Kakasheka Usman ya bayyana cewa “Sojojin Najeriya na rundunar Task Force na 155, Brigade ta 21 sun gudanar da aiki inda kori yan Boko Haram da suka rage a garuwan Dipcheri, Jere, da kuma Cholgo.
Motar da yan kungiyar suka gudu suka bari
Sojojin sun share duka garuruwan daga tsagerun ba tare da wata matsala ba inda suka kama wasu wadanda ake zargi guda 2.
Yan ta’addan kuma sun gudu sun bar mota guda 1, keke da kuma bindiga harlba ruga guda 2. Wannan aiki da akayi yana cikin tsarin zaman lafiya dole domin a kauda yan ta’addan daga yankin.
Bindigogin yan kungiyar
Jama’a su cigaba da taimakon mu da bayanai domin dakila dukkan aiyuka yan ta’addan. Mun gode maku da gudunmuwar ku.
Wanni wanda aka kama wanda ake zargin dan kungiyar Boko Haram ne
Idan za’a iya tunawa, a makon daya wuce kasar Kamaru ta kama wani kwamandan yan Boko Haram a kuduncin kasar.
Wani wanda ake zargin dan Boko Haram ne
A wani labarin kuma, yar kunar bakin waken da aka kama wadda ta bayyana cewa ita yar Chibok ce na cigaba da samun kulawa ta musamman. Gwamnatin Najeriya tuni ta aika da tawaga domin tantance bayanai.
The post Sojojin Najeriya sun fatattaki yan Boko Haram a Jere appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us