Sports Betting

Trending

random

Yan sanda sun kama wasu yan Boko haram guda 2

– Yan sanda sun kama kwamandojin Boko Haram guda 2

– An mika su ga sojojin Najeriya a Yobe

– Yan sanda sun bukaci mutane dasu taimaka masu

wadanda yan boko haram

Yan ta’addan Boko Haram

Rundunar yan sandan Najeriya dake Taraba ta kama wasu kwamandojin Boko Haram guda 2 inda ta mika hannun sojoji a jihar Taraba.

Daya daga cikin su mai suna  Ali Audu an kama shine a Tella, karamar hukumar Gassol, shi kuma gudan, Abdulmumini Abdullahi an kama shine a karamar hukumar Balli.

Kamfanin Daillancin labaran Najeriya ta jihar Taraba, (NAN), ta bayyana cewa Kwamishinan Yan sandar Jihar, Shaba Alkali ne ya bayyana haka a ranar Laraba inda yake ganawa da yan Jarida.

KU KARANTA: 

Ya bayyana cewa sun mika su ga hannun sojoji a jihar Yobe. “Mun kama tabbatattun yan Boko Haram guda 2 a kananan hukumomin Gassol da Balli.

Kwamishina yan sandan kuma ya sha alwashin kawo karshen rikicin da akayi a karamar hukumar Ibi. Ya bayyana cewa rundunar yan sandan jihar ta kai jami’an ta dayawa domin hana rikicin.

A wani labarin kuma, shugaba kasa Muhammadu Buhari ya bada umurni sojojin ruwa na Najeriya dasu kafa Bariki a wajen Tabkin Chadi. Ana tsammanin hakan zaya taimaka kwarai wajen kare Najeriya da taimakawa wajen yaki da ta’addanci

The post Yan sanda sun kama wasu yan Boko haram guda 2 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


Yan sanda sun kama wasu yan Boko haram guda 2 Reviewed by Olusola Bodunde on 23:33 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.