Sports Betting

Trending

random

Da tuni na aje mukami na inda ni Saraki ne – Sanata Buhari

– Sanata Abdulfatai Tayo Buhari ya bayyana cewa inda shi saraki ne da yayi murabus

– Sanata Buhari wanda shine ciyaman na kwamitin ICT a majalisa ya bayyana cewa bai kamata Saraki ya cigabada zama shugaban Majalisa ba

– Sanatan ya nemi Saraki ya kwaikwayi Firayim Ministan kasar Iceland wanda ya sauka saboda ana zarginn shi

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a kotun CCT

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a kotun CCT

Akwai alamu cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki yana fuskanatar rikici akan cigaba da zama shugaban majalisar. Bayan kiran da Sanata Abdulfatai, wanda ke wakiltar Oyo ta kudu yayi mashi da yayi murabus, wata kungiya mai suna kawance akan fidda shugabannin banza ta nemi Saraki da yayi murabus kada ya tozarta kujerar shugaban majalisa.

Inda yake magantawa akan lamurra, Sanata Buhatri ya bayyana cewa ” Ban cika so in maganta ba akan rayuwar mutane, amma inda nine ake bincika, da nayi murabus kamar yadda shugaban kasar Iceland yayi murabus.

Sanatan kuma ya bayyana cewa gwamnatin Buhari zatayi iya bakin kokarin ta wajen ganin cewa ta cika alkwurran da akayi ma jama’a a lokacin yakin neman zabe a 2015.

Inda yake bada hakuri a madadin jam’iyyar shi, Sanata Buhari ya bayyana cewa ” Muna sane da halin da yan Najeriya suke ciki. Babu wanda yayi tsammanin abubuwa sun lalace kamar haka. Zamuyi iya bakin kokarin mu. Baza mu matsa ma yan Najeriya ba.

Inda kuma yake magantawa akan karancin man fetur, Santa Buhari ya bayyana cewa ” Mun shiga haka ne saboda rashin kula irin namu. Inda muna gyara matatun kamar yadda ya kamata, da bamu shiga haka ba.

The post Da tuni na aje mukami na inda ni Saraki ne – Sanata Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


Da tuni na aje mukami na inda ni Saraki ne – Sanata Buhari Reviewed by Olusola Bodunde on 09:53 Rating: 5
All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.