Dole in mutu in hadu da Ubangiji na – Babangida
– Tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida ya musanta cewa ya mutu
– Ya bayyana cewa yana fama da rashin lafiya amma ba kwance yake ba
– Baban gida ya bayyana cewa yana fama da wani ciwo da yaji tun yakin basasa
Ibrahim Babangida
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Ibrahim Babangida, ya bayyana musanta cewa ya mutu. A jiya ne Lahadi 24 ga watan Afrillu ya bayyana hakan inda yake tattana da wasu yan jarida a gidan shi dake Jihar Nija.
KU KARANTA: Gobara ta kama a gidan Mai na NNPC dake a Kaduna
Kwanakin baya wasu rahotanni suka fito inda wasu ke cewa Ibrahim Babangida baya da lafiya kuna yana cikin tsananin rashin lafiya a wancan lokacin.
Babangida yace ” Eh gaskiya ne bana jin dadi wanda hakan ya sanya na rage shiga tarukan jama’a. Amma fa ba wai banda lafiya bane ta yadda za’a ce bana iya yima kai na komai.
” Ni abun baya damu na. Nasan dole ne in mutu inje in hadu da Ubangiji na.
” Babu wani abu wanda zaya daga ma mutum hankali.
” A matsayina na musulmi, Addini na ya riga ya fada mani.
” Zaya iya zama yanzu, ko kuma shekaru 100 masu zuwa. Zaya iya zama nan da kwanaki 2.
” Zaku iya gani muna ta gaisawa da jama’a. Nan da mintuna kadan kuma duka zamuje muyi sallah sai muje mu ci abinci. Daga nan sai inje inyi baccin rana.
“Babu wanda yafi karfin yayi rashin lafiya, domin babu wanda zaya iya wuce abunda Allah ya kaddara mashi.
Inda yake magantawa akan Najeriya, IBB ya bayyana cewa mutanen Najeriya nada kokari, jajircewa da kwazo.
Ya bayyana cewa najeriya nada kyakkyawon gaba.
Babangida kuma ya maganta akan wani ciwo da yaji sakamakon halbin shi da harsashi da akayi lokacin basasa. Sannan ya bayyana cewa a lokacin da yake shugaban kasa, yayi tafiya yaje kasar Jamus inda aka yi mashi aiki, wannan ya sanya ciwon yake tasowa lokaci-lokaci.
The post Dole in mutu in hadu da Ubangiji na – Babangida appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us