Gobara ta kama a gidan Mai na NNPC a kaduna
– Wata gobara ta kama a gidan mai na NNPC dake a Kaduna
– Mutane 3 sun rasa rayukan su
-Motoci 15 sun kone
Sakamakon wata gobara data kama a wani gidan Mai na NNPC dake a Kaduna, mutane 6 sun rasa rayukan su inda motoci15 suka kone ta yadda baza ka iya shaida su ba.
Jaridar The Breaking Times ta bayyana cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe 5:09 na yamma inda tayi taci har bayan awanni 3 da farawar ta.
Mataimakin gidan Man na Fasada ya, Alhaji Jibril Musa, ya bayyana cewa a ranar Asabar ne a lokacin da wata mota ke saukar da mai sai ta kama da wuta inda ta kone kurmus.
“Ba’a sanya ma man sosai ba.Bayan da Man ya zuba a kasa, wani Mai mota ya gama shan man nashi inda yana kunna motar shi sai gobarar ta fara.
” Motoci 15 ne suka kone inda gobarar ta shafi gidan Mai na kusa damu. Yan kwana-kwana sunzo inda suka fara kokarin kashe wutar.
Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya ya bayyana cewa, wani mai bada shaida ya bayyana cewa, gidan mai na kusa na Shammaco shime ya kama da wuta.
Inusa yace “gobarar ta aiku kuma mu babu abunda zamu iya yi. Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukan su, Allah yaba wadanda suka ji raunuka lafiya.
Inda aka tuntubi shugaban hukumar Yan Kwana-kwana ta jihar Kduna, Paul Abio, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa ma’aikatan hukumar sunyi kokarin kashe wutar.
Alhaji Babangida Kinkinau shima ya bayyana cewa gobarar ta auku ne a lokacin da ake kokarin sauke man.
The post Gobara ta kama a gidan Mai na NNPC a kaduna appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us