Ku karanta abinda Gwamnonin Arewacin Najeriya ce game da Buhari, yan Boko Haram
– Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake samu jinjina daga mutane daban-daban saboda kokarinshi da murkushe kungiyar yan ta’addan Boko Haram a Arewa maso gabashin Najeriya tun zamani an ranstar da shi a Badi
– Wasu Gwamnonin Arewacin kasa suna cikin mutane wadanda suke yabawa shugaban kasan akan abunda yake yi da karshe halin ta’addanci
Ibrahim Ammani, wani dan jaridai dake jihar Kaduna, ya ruwaito wanda Gwamnonin Arewa sun yi jinjina ta musanman ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda sakamakon nasarar da aka samu akan ta’addancin Boko Haram.
Shugaban kasar Najeriya mai suna Muhammadu Buhari
Kungiyar Gwamnonin Arewa, karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar, kuma Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, sun yi jinjina ta musanmam ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, sakamakon gagarumar nasarar da gwamnatinsa ta samu wajen dakushe kaifin Boko Haram
KU KARANTA KUMA: Babu abun kamar lura a kasashen waje – Buhari
Gwamnonin na Arewa sun yi wannan yabon ne, a yayin zaman taron da Kungiyar ta su ta yi a gidan Gwamnatin jihar Kaduna na Hassan Katsina dake tsakiyar garin Kaduna.
Wasu Gwamnonin Arewacin kasar Najeriyaid=”fbPhotoSnowliftCaption” class=”fbPhotosPhotoCaption” tabindex=”0″ data-ft=”{“tn”:”K”}”>
Haka nan, kungiyar Gwamnonin sun tabo batutuwa wadanda suka shafi rikice-rikice dake addabar Arewa, wadanda suka hada da fashi da makami, satar shanu, garkuwa da mutane da kuma rikicin manoma da makiyaya, inda suka yi alkawarin yin dukkanin mai yiyuwa wajen shawo kan wadannan matsaloli.
Gwamnonin na Arewa sun koka dangane da yadda kayayyakin gadon Arewa da Sardauna ya samar suka balbalce a yankin, kamar Bankin Arewa, Kamfanin Jaridar New Nigeria, da Kamfanin hada-hada na Arewa NNDC, Masakar Kaduna da sauran abubuwa masu yawa, wadanda rashin su ya haifar da koma baya da rashin aiki ga Matasan Arewa.
Gwamnonin sun kuma saurari rahotanni daga bakin wasu Kwamitoci da suka kafa a zamansu na baya, musamman Kwamitin Kwamishinonin Shari’a na jihohi 19 dake yankin, wanda zaiyi gyaran fuska akan tsofaffin dokokin da ake dasu akan manyan laifuka.
Hankalin Kungiyar Gwamnonin ya dawo kan yadda bakin Akidu na musulunci suke shigowa yankin daga wasu kasashe, inda suka tabbatar da cewar zasu dauki matakan bibiyar dukkanin wata Kungiyar addini mai rijista da mara rijista, domin gano ainihin me take yi, sannan za su wajabta tantance dukkanin wani mai wa’azi ta hanyar bada lasisi, da kuma tabbatar da cewar dukkanin makarantun Islamiyya sun yi rijista da gwamnati, da fatattaka gami da kulle makarantun da ba su da rijista.
The post Ku karanta abinda Gwamnonin Arewacin Najeriya ce game da Buhari, yan Boko Haram appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us