Ministocin Jonathan zasu bar PDP saboda Sheriff
– Tsofaffin Ministocin a karkashin tsohon shugaban kasa Jonathan sun bayyana cewa basu amince da Sheriff ba
– Sun bayyana cewa shi ba mutum bane wanda za’a iya amincewa dashi
ShugabanJam’iyyar PDP Sanata Ali Modu Sheriff
Tsofaffin Ministocin na tsohon shugaban kasa Jonathan, sunyi barazanar barin jam’iyyar PDP saboda basu amince da shugaban jam’iyyar na rikon kwarya ba, Ali Modu Sheriff. Sun bayyana cewa yadda abubuwa ke tafiya ayanzu, Sheriff na shirin maida kanshi shugaban jam’iyyar ne.
KU KARANTA: Dole in mutu in hadu da Ubangiji na – Babangida
Rahotanni a baya baya sun nuna cewa Ali Modu Sheriff na shirin maida kanshi shugaban jam’iyyar na din-din-din inda zaya cigaba da kasancewa hakan sai zuwa 2018 sai ya aje mukamin inda zayayi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyar. Rahotan ya nuna cewa wasu gwamnoni na jam’iyyar PDP din na goyon bayan shi.
A cewar jaridar The Punch, tsofaffin Ministocin sun gana a ranar 21 ga watan Afrillu a Birnin Tarayya Abujainda suka tattauna akan jam’iyyar da kuma a kan shirin zaben shugaban jam’iyyar. Shugaban kwamitin rarraba mukamai, Gwamna Udom Emmanuel, ya bayyana cewa kwamitin ya bada kujerar shugabancin kasar zuwa Arewa Maso Gabas.
Sheriff shima daga Arewa maso Gabas yake.
KU KARANTA: Gobara ta kama a gidan Mai na NNPC dake a Kaduna
Wani Minista wanda baya so a sanya sunan shi yace “Ina mamaki yadda wasu abokan mu ke kokarin kare Sheriff duk da matsayar da muka dauka tare a kwanakin baya.
” Wasu sunce a sake bashi dama, domin kada mutane suga kamar muna kin shine a matsayin shi na mutum.
” Da yawan mu dai dama mun riga mun fada masu, idan dai aka maida Sheriff toh mu fita zamuyi. Don ba dole bane mu tsaya a jam’iyyar PDP.
Da rin wadannan barazanar da ake samu, Shugaban Kwamitin sasanci wanda yake samun shugabanci daga Sakataren kungiyar na kasa, Farfesa Wale Oladipo, ya bayyana cewa sun ta kokarin sasanci a tsakanin manbobin kungiyar.
The post Ministocin Jonathan zasu bar PDP saboda Sheriff appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us