Abun mai ban tausayi: Uwar Sanata Shehu Sani ta rasu bayan dogon ciwo (hotuna)
– Wani Sanata wanda yake yaki na hakkin bil adama daga jihar Kaduna ta tsakiya mai suna Shehu Sani ya rashu mamanshi saboda dogon rashin lafiya
– Fatima Abubakar Sani mahaifiyar wani Sanata ta mutu a yar shekaru 72, inda tana da yara guda biyar da jikoki guda 20
– Wani dan jarida mai suna Ibrahim Ammani wanda yake ruwaito daga jihar Kaduna ya rahoto wanda Allah ya yi wa uwar Sanata Shehu Sani rasuwa
Rahotanni na nuna cewa wanda, da safiyar ranar Asabar din nan ne Allah ya yi wa Hajiya Fatima Sani, mahaifiyar Sanata Shehu Sani rasuwa.
KU KARANTA KUMA: An bayyana akan cire tallafin man fetur
Hajiya Fatima wacce ake yi wa lakabi da sunan Kyauta, ta rasu ne bayan rashin lafiya da ta yi fama da ita, kuma tuni aka yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Ga hotunan a kasa:
Hajiya Fatima Abubakar Sani, wata uwar Sanata Shehu Sani kafin ta rasu
Hajiya Fatima Sani da yaranta kafin rasuwarta, anan kuma akwai Sanata Shehu Sani a hannun dama farkon
Sanata Shehu Sani inda yake yi magana da wani dan jarida daga Gidan Talabijin ta NTA, Akwai mutane da yawa a bayan wani Sanata wadanda suka zo saboda ta’aziyya
Yan jihar Kaduna wadanda suka jajanta da Sanata Shehu Sani suna da yawa
The post Abun mai ban tausayi: Uwar Sanata Shehu Sani ta rasu bayan dogon ciwo (hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us