Sports Betting

Trending

random

Badakalar kudi: Minista na fuskantar tuhuma daga Buhari

A wani rahoto da jaridar Thisday ta rawaito, ta bayyana cewa shugaba Buhari ya na tuhumar ministan shari’a na kasa Abubakar Malami a kan wasu laifuffuka da aka danganta shi dasu.

201x263xAbubakar-Malami.jpg.pagespeed.ic.fpc9IjU0MN

A Takardar tuhumar, shugaban ya bukaci ministan da ya fadi albarkacin bakin sa a kan tuhumar da ake masa na shagulatin bangaro da batun da ya shafi wasu kudade da suka kai har naira biliyan 300 da suke boye a wasu bankunan Nigeria.

Wani Dr George Uboh, shugaban wani kanfanin tsaro mai suna Panic Alert Security System (PASS) shi ne ya janyo hankalin shugaban kasa Buhari ga wannan al’amari ta hanyar wasu wasikokin kokawa guda biyu da suka turawa shugban a inda suke tuhumar Malami da lalata kokarin sun na fito da kudaden da aka riga aka san inda suke

Malami dai ya karyata tuhumar da ake masa kuma ya kara da jaddada tsayuwar sa wajen gano satattun kudade da kuma mayar da su inda ya kamata kamar yanda gwamnatin shugaba Buharin ta bukata.

Ya kara da cewa wannan tuhumar ta biyo bayan janyewar damar da ya bawa Uboh ta gano kudaden saboda ya ga ya fara wuce gona da iri. Ya bayyan cewa tuhumar ta Uboh ta karya ce kuma bata da makama. Wannan yana kunshe ne a cikin takardar Martani da ya aika wa shugaba Buhari ranar Litinin, 4 ga watan afrilun bana mai number HAGF/SH/2016/Vol.1/20

Agafe guda kuma, shugaba Buhari ya kusa bayyana daidai adadin kudin da gwannatin sa ta karba daga hannun wadanda aka tuhuma da badakala da tattalin arzikin kasa. Rahoton ya bayyana cewa shugaban zai bayyana hakan ne a taron yaki da rashawa da za’ayi a birnin London wanda zai halarta a kwanan nan.

A wani labarin kuma, a gobe ne shugaba Buhari zaya halarci taron yaki da rashawa wanda za’a gudanar a birnin Landan, Kasar Ingila.

The post Badakalar kudi: Minista na fuskantar tuhuma daga Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).


Badakalar kudi: Minista na fuskantar tuhuma daga Buhari Reviewed by Olusola Bodunde on 15:12 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.