Ga abunda aka samu Shugaba Buhari yana yi maimakon ace ya ziyarci jihar Legas (hotuna)
A yau ranar Litinin, 23 ga watan Mayu, an ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da gwamnan jahar Ogun Ibikunle Amosun, A yayin da ya kamata ace ya kai ziyara zuwa jIhar legas.
A hotunan da muka samu daga wakilan jaridan Sahara Reporters ya nuna cewa Shugaba Buhari, yace yana fama da ciwon kunne, abunda ya zamo abun ban dariya yayin da gwamnan jihar Ogun ya ziyarce shi.
KU KARANTA KUMA: Uwargidan gwamnan jihar Ogun ta maganta kan Musulunci
Ya fasa tafiyar da ya kamata yayi a ranar lahadi, 22 ga watan mayu zuwa jahar legas, sakamakon wani larura tashi, abu na farko da ya taba faruwa ga shugaban kasa fiye da shekaru 15. Inda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya hallarci taron a jihar legas kuma ya bada tallafin gaggawa a jihar.
Akwai korafi na cewa shugaban kasa Buhari ya soke ziyaran shi zuwa jihar ne saboda yana sauraron ziyarar gwamnar jahar ogun .a lokacin da ake hada wanna rahotanin, bazamu iya kawo muhimman hujar dalilin ziyarar gwamnan ba zuwa ga fadar shugaban kasa ba.
A wani rahoto a mako da ya wuce ne gwamnatin tarayya a karkashin Shugaba Buhari ta sanad yadda za’a kashe wa Naira Biliyan 350 wajen gina tituna guda 14 a fadin kasar nan.
Ku duba wasu hotunan kan ziyarar gwamnan jihar Ogun a fadar shugaban kasa dake Abuja, wani babban birnin kasar Najeriya a kasa:
Shugaban kasa Muhammadu Buhari inda yake tattauna da wani bakoncin gwamna mai suna Ibikunle Amosun da kuma wani manyan ma’aikaci a fadar shugaban kasa mai suna Abba Kyari
Shugaba Muhammadu Buhari yake dariya da wani gwamnan jihar Ogun mai suna Sanata Ibikunle Amosun
Acikin mukamin Shugaba Buhari
Shugaba Buhari da Gwamna Amosun
The post Ga abunda aka samu Shugaba Buhari yana yi maimakon ace ya ziyarci jihar Legas (hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us