Sports Betting

Trending

random

Ku karanta abunda yake faruwa cikin wasu jaridun Najeriya a yau, Litinin

– Wani dan jarida mai suna Muhammad Musa Kawuwale Potiskum ya rubuto kan sharhin jaridun Najeriya a yau Litinin, 23 ga watan Mayu

– Akwai abubuwa daban-daban wadanda suke faruwa a kasar Najeriya

Acikin jaridar This Day, a yau Litinin shugaba Buhari zai kai ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar Lagas, amma wata sanarwa tace shugaban ya fasa zuwa, Mataimakinsa Yemi Osibanjo ne zai wakilce shi.

Jaridar The Nation ta ruwaito wanda, kungiyar kwadago mai suna NLC ta janye yajin aikin da ta fara a ranar Larabar makon jiya, wanda bai sami karbuwa ba, saboda cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi

KU KARANTA KUMA:

A Vanguard, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai adawa ta rabe gida biyu bayan ta gudanar da babban taron ta na kasa kashi biyu, daya a Abuja daya kuma a Pdan zaben shugabanni

Nigerian Tribune ta rahoto wanda, wata kotu ta bada umurnin a binciki tsohon shugaban kasa Jonathan da tsohuwar ministar kudi Ngozi saboda bacewar wasu kudi tiriliyan 30 a lokacin mulkinsu.

Inda jaridar The Guardian ta rahoto wanda wani likita ya gargadi ma‘aikatar lafiya ta kasa da ta gaggauta daukar matakin rigakafi akan cutar Zika, wadda ta bulla a Nahiyar Afrika a karon farko, wadda ake samunta daga cizon sauro

The Punch ta rubuto wanda, Hukumar kula da kayyade farashin mai DPR ta gargadi ‘yan kasuwar mai masu zaman kansu IPMAN da su guji kara farashin mai fiye da 145 akan kowace lita

A karshe jaridar Leadership ta ruwaito wanda Shugaban ‘yan sanda na kasa mai suna Sifeton Janar Solomon Arase ya jibge jami‘an tsaro a hedikwatar sakatariyar PDP saboda tsoron tada rikicin tsakanin bangarorin PDP da kowa yake ikirarin shine halastaccen shugaban PDP na kasa.

The post Ku karanta abunda yake faruwa cikin wasu jaridun Najeriya a yau, Litinin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).


Ku karanta abunda yake faruwa cikin wasu jaridun Najeriya a yau, Litinin Reviewed by Olusola Bodunde on 12:17 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.