Buhari ya bayyana abu na farko da zaiyi wa yan Najeriya
-Masana sunyi kira ga sake fasalin al’amuran tattalin arziki tun wani lokaci mai tsawo da ya wuce
-Danyan man fetur shine babban abunda ke kawo ma kasar kudi
-Shugaban kasa Buhari yace harkan noma shine abu na farko da gwamnatinsa ta sa a gaba
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gamnatinsa zata ci gaba da ba harkan noma fiffiko, saboda muhimmancin sa. Shugaban kasa Buhari yace wannan zai yiwu ne ta hanyar shirye-shirye da kuma manufofin da aka tsara domin bay an Najeriya karfin gwiwa, saboda a samar da isasshen abincin da za’a ciyar da kasar.
Shugaban kasa ya bayyana hakan ne a taron bankwana da Hoang Ngoc Ho, Ambasadan jumhuryyar Vietnam mai wucewa a ranar Talata, 9 ga watan Augusta a fadar shugaban kasa dake Abuja.
KU KARANTA KUMA: EFCC sun fara bincike a kan arigizon kasafin kudi
Bugu da kari, ya taya Vietnam murna da yayi zaben al’amura mafi inganci da ya jagoranci Najeriya ta ciyar da kanta da duniya. Haka zalika, Ambasada Ho ya nuna jin dadinsa da ci gaba da ya rubuta a tsakanin kasar Vietnam da kasar Najeriya. Ambasadan ya lura da hadin kan da jihohin Najeriya a fannin Noma, wanda ke samun ci gaba.
Ambasadan Vietnamese ya bayyana cewa Vitnam a shirye take da taka rawar gani a cikin sake fasalin al’amuran tattalin arzikin gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Buhari. Domin kawo ci gaba a fannin noma na kasar, a satin da ya wuce, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata hana shigo da shinkafa kasar Najeriya a shekara ta 2019.
The post Buhari ya bayyana abu na farko da zaiyi wa yan Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us