Muhammadu Buhari ya hadu da Dogara da Bakare aganawa ta sirri.
–Shugaba Buhari ya gana da kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara.
–Buhari ya gana da Dogara da fasto Tunde Bakare a gidan shugaban kasa dake Abuja
–Dogara yya tafi Aso rock tare da wasu yan majalisa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hadu da shugaban majalisar wakilai ranar juma’a ganawa ta sirri. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hadu da Yakubu Dogara da Tunde Bakare a ganawa ta sirri.
Haka ma Buhari ya gana da shugaba mai kula da coci mai suna Later Assembly, fasto Tunde Bakare a gidan shugaban kasa da ke Abuja.
Jaridar Nation ta ruwaito cewa ganawar da sukayi da Dogara wanda sukayi a ofishin shugaban kasa da ke Abuja, inda ya tsawaita har tsawon awa 1. Shugaban ya samu rakiyar wadansu yan majalisa wanda ya hada da sanata Suleman Nazif Bauchi. Ganawar ta juma’a it ace ganawa ta 2 a sati 2 tsakanin Dogara da Buhari.
Shugaban majalisar yaki amsa ma yan jarida tambayoyinsu bayan kamala taron. Fasto Bakare shine wanda suka fito takara tare da Buhari a zabe na 2011. Har yanzu suna ganawa yayin da muke tattara rohoton.
The post Muhammadu Buhari ya hadu da Dogara da Bakare aganawa ta sirri. appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us