Sports Betting

Trending

random

Rio Olympics: Sharhin gabanin wasan Najeriya da Colombia 

Kungiyoyi biyo na rukunin ‘B’ a gasar kwallon kafar cin lambar Zinarin Olympics da ake bugawa a kasar Brazil watau Najeriya da takwarar ta ta Colombia zasu kara a yau 10 ga watan Agusta din a filin wasa na Corinthians a garin Sao Paulo.

Olympics Nij

Ita dai kasar Najeriya yanzu haka tana da tabbacin buga zagaye na gaba na gasar don kuwa ta lashe wasannin ta 2 da ta buga a baya sai dai kuma zata so ta sake doke Colombia din domin samun maki 9 don kaucewa haduwa da wasu da sukayi na daya a wani rukunin.

Tuni ma dai dan wasan Najeriya kuma mai bugawa kungiyar Chelsea John Obi ya tabbatar wa da duniya cewar ko kusa ba zasu dauki wasan da sauki ba.

Duk kuwa da cewar mai horar da kungiyar kwallon ta Najeriya Samson Siasia ya ce zai hutar da wasu daga cikin yan wasan sa ba zasu buga gasar ba amma kuma yace duk da haka kungiyar tana da yan wasan da zasu iya doke duk wata kungiya dake a cikin gasar ma.

Mai horar war yace: “zan hutar da wasu yan wasa na don akwai yiwuwar a je wasan karin lokaci a zagaye na gaba na wasan to amma fa ba wai zamuyi wasa ne ba a wannan wasan namu na gaba.

“Yanzu haka dai ina da tawagar yan wasa cike da kwararru wadan da zasu iya karawa kuma su doke ko wace kasa dake a cikin gasar.”

Su kuma a dayan hannu dai kasar Colombia suna biye ne da kasar Najeriya din da maki 4 a jadawalin rukulin ‘B’. Kasar kuma tana taka leda ne sosai kuma abin sha’awa. Kawo yanzu kuma daman kasar ta Columbiya ta buga kunnen doki ne da sauran kasashen biyu dake a cikin rukunin na Japan da Sweden. Haka nan kuma suna da wani shahararren dan kwalon su na gaba mai suna Teofilo Gutierrez. Za dai a buga wasan ne a karfe 11pm na daren yau kuma Naij.com zata ci gaba da baku yadda zata kaya.

The post Rio Olympics: Sharhin gabanin wasan Najeriya da Colombia  appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Rio Olympics: Sharhin gabanin wasan Najeriya da Colombia  Reviewed by Olusola Bodunde on 16:36 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.