Rio Olympics: Yan Najeriya 3 sun kafa tarihi a gasar
Dai-dai lokacin da yan kasar nan ke kuka game da rashin isasshen shirin da tawagar kasar Najeriya tayi wa gasar Olympics da ke gudana yanzu a garin Rio dake kasar Brazil, kawo yanzu dai yan Najeriya 3 ne suka nuna hazakar gaske a gasar a fannoni da dama.
Chierika Ukogu na daya daga cikin su. Ita dai wannan tana wakintar kasar ne a wajen wasan tseren kwale-kwalen ruwa. Sauran sun hada da shahararren dan wasan kwallon tebur Aruna Quadri da kuma Segun Toriola.
Shi dai Toriola yanzu haka yana zaman dan wasan da yafi kowa zuwa gasar ta olympics ne bayan da yaje a karo na 7 yanzu.
Segun Toriola
Shima dai Quadri ya kafa wani tarihin a gasar a matsayin sa na dan nahiyar Afrika na farko da ya samu nasarar zuwa zagaye na kusa da kusa da na karshe bayan da ya doke wani dan kasar Germany wanda kuma ke zaman na 7 a jerin wanda yafi kowa iya wasar tebur din a duniya.
Haka zalika ma dai cikin wadanda suka kafa tarihin hadda Ukogu wadda yake zuwan ta ne na farko a gasar amma kuma tayi nasara a fagen tseren kwale-kwalen ruwan agin mata masu yi su kadai.
Aruna Quadri
Da yake zantawa da yan jarida, Aruna Quadri yace: “Ina mai matukar murna da na zama cikin daya daga manyan yan wasan tebur a duniya. Na ji dadi kuma da na samu damar zuwa zagaye na 4 a gasar da kuma nasarar da na sau a kan wadan da ke a matsayi na 7 da kuma 13 a wajen iya gasar a duniya.
The post Rio Olympics: Yan Najeriya 3 sun kafa tarihi a gasar appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us