Wutan lantarki ya kashe ma’aikacin KERDCO a jihar Kano
-Wutan Lantarki ya kashe wani ma’aikacin kamfanin wutan lantarki na jihar kano wato, Kano Electricity Distribution Company (KERDCO)
-marigayin mai suna Usaini Usman ya mutu bayan ya hadu da wayan wutan lantarki
Wani ma’aikaci a KERDCO mai suna Usaini Usman ya mutu sanadiyan wutan lantarki a jihar Kano.
Bisa ga rahotanni, Usman mai shekaru 37 a duniya, ya mutu sanadiyan wutan Lantarki, a jiya 18 ga watan Augusta, bayan kan say a hadu da wani wayan wutan lantarki a makarantar kolegin tarayya.
An rahoto cewa yana cire wani wayan wuta ne a lokacin da al’amarin ya afku.
Majiyar ta bayyana cewa an kais hi babban asibitin Murtala Muhammed inda aka tabbatar da mutuwar sa.
Haka kuma, a ranar Juma’a, 12 ga watan Augusta kamfanin nan mai suna Transmission Company of Nigeria (TCN) ta bayyana cewa wani wutan lantarki ta ja wani mai lalata wayoyi a Shiroro/ Tegina/Kontagora karfin wutan 132 KV.
KU KARANTA KUMA: APC kawai ce zata ceci Saraki- Sanata Marafa
Ganar Manaja dake kula da al’amura jama’a, Seun Olagunju a wani sanarwa ya bayyana ainahin abunda ya faru. Olagunju yace wanda ya bata yayi nasarar yanke wayar dake tower 187 sannan ya koma na Tower 188 ta gurin da wayan wutan yake. Ainahin lokacin da abun ya faru a daren ranar Litinin, 1 ga watan Augusta lokacin da wanda ake zargin ya bata yake “ida nufin sa” a kusa da wayan wutan.
The post Wutan lantarki ya kashe ma’aikacin KERDCO a jihar Kano appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us