Sports Betting

Trending

random

An yanke wa dan Najeriya da aka kama da hodar iblis hukunci a Dubai

– An cafke wani dan Najeriya mai fataucin miyagun kwayoyi

– Ya adiyi hodar iblis ne a kwaya amman an dawo da hodar iblis din bayan likta yayi mai aiki

– An tura wanda ake zargin gidan kurkuku

An yanke wa wani mutumin kasar Najeriya hukunci a kasar Dubai bayan an kama shi da kwayoyin hodar iblis guda 100 a cikin sa.

A cewar Khaleej Times, an kama dan Najeriyan ne filin jirgin saman kasar Dubai a watan Afrilu.

Wani dan sanda wanda ya kasance a dakin aikin ya bayyana yadda Likitoci suka fito da kwayoyin hodar iblis guda 100 da aka boye a cikin  wanda ake zargin.

KU KARANTA KUMA: Yan kauye sunyi watsi da wata mata mai ciwon kafa

“An umarceni da na tsaya gadin wanda ake zargin a asibiti. Jami’an yan sandan filin jirgin saman ne suka tura shi can din bayan an zarge shi da fataucin miyagun kwayoyi a cikin sa.

“An samu yawan kwayoyin hodar iblis guda 100 a cikinsa. Na kwace na kuma mika su ga hukumar masu kula da masu fataucin miyagun kwayoyi,” cewar sanarwar

Kotu ta kama shi da aikata laifin da ake zargin sa a kai,ta kuma umarce shi da ya biya tara na kimanin Dh 100,000 kudin kasar su.

An hukunta shi kan laifin fataucin miyagun kwayoyi ta hanyar yanke mai zaman gidan yari na shekaru 10.

The post An yanke wa dan Najeriya da aka kama da hodar iblis hukunci a Dubai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


An yanke wa dan Najeriya da aka kama da hodar iblis hukunci a Dubai Reviewed by Olusola Bodunde on 05:39 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.