Sports Betting

Trending

random

Mutane 8 sun rasu a hadarin mota a jihar Ebonyi

– Wata hadari ta faru a Iyere Edda Afikpo a jihar Ebonyi wanda yayi sanadiyar mutuwan mutane 8

– Fasinjoji da dama sun samu raunuka ir-iri a hadarin

– An jingina hadarin ga wani direban motan EBOTRANS, wanda ya fita hayacin shi

Scene-of-an-accident

Mutane 8 ne suka rasa rayukansu sanadiyar hadarin mota, wanda wani direban motan hayan EBOTRANS ya fita hayacin shi kuma motan tayi kundunbala a Iyere Edda a karamar hukumar Afikpo da ke jihar Ebonyi.

Jaridar New Telegraph ta bada rahoton cewa mutane 7 ne suka mutu a take kuma 1 ya karasa numfashinsa a asibbiti. Sauran fasinjojin sun ji raunika daban-daban.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun afka gidan talabijin NTA a Onitsha

Game da wata idon shaida, Iheanacho Okam,wanda yake mazaunin unguwan, yace motan na dawowa daga Aba a jihar Abiya yayinda hadarin ya faru.

Okam: “ An Fasinjojin da suka samu rauni asibiti a Ekoli Edda a yankin,sauran kuma an kaisu asibiti Owutu Edda domin jinya. An kai gawawwakin wadanda suka rasa rayukansu dakin gawawwakin asibitin Owutu Edda.

Okam yace jami’an hukumar kula da tsaron hanyoyi FRSC basu zo wurin ba sai dai yan sanda da suka zo da motocinsu.

A wata labara mai kama da haka jami’in hukumar kula da tsaron hanyoyi FRSC Corps Marshal, Boboye Oyeyemi,yayi gargadi gay an najeriya da su sanya na’uran rage gudu a motocinsu. Musamman masu motan haya saboda sabawa doka.

The post Mutane 8 sun rasu a hadarin mota a jihar Ebonyi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Mutane 8 sun rasu a hadarin mota a jihar Ebonyi Reviewed by Olusola Bodunde on 07:39 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.