Zan samar da wuta mai karfin 450mw a Edo – Obaseki
Dan takarar jam’yyar APC na zaben gwamnan jihar Edo dake karatowa Mista Godwin Obaseki yayi alkawarin samar da wutan lantarki da karfinsa ya kai ‘mega watt 450’ a shekarar 2017.
Dan takarar ya bayyana haka ne a yayin da yake ma wakilan al’ummar kabilar Ibo mazauna Bini jawabi a ranar laraba 14 ga watan satumba, inda yace za’a samar da wutan ne daga kamfanin na’urar sama da wutan lantarki Azura Power Plant wanda gwamnatin APC mai ci a yanzu ta kawo jiyar.
KU KARANTA: PDP ta kai karan Obaseki Kotu
Jaridar Vanguard ta ruwaito Obaseki yana cewa idan aka kammala aikin gina kamfanin, wutan lantarkin zai kara yawan hadahadan kasuwanci tare da samar da karin kananan masana’antu.
Sa’annan ya kara nanata burinsa na samar da ayyukan 200,000 tare da bunkasa harkar noma a jihar idan har an zabe shi. “mun wuce zamanin siyasar raba kudi, yanzu muna zamanin siyasan cigaba ne. kudin mai ya karye, kuma babu shi ma, balle a rabar, don haka ya kamata a zabi shugaba da zai samar da hanyoyin samun kud daban daga mai. “idan muka bunkasa harkar noma, kasuwanci zai habbaka, tare da karin 450mw na wuta daga Azura Power Plant” inji shi.
Obaseki yayi nuni da cewa samun yawaitan kasuwanci zai samar da karin ayyukan yi, wanda da haka za’a samu karin arziki da kuma karin kudaden shiga, yace wannan shi ne abinda siyasan cigaba ya kunsa. Ya kara da cewa daga zaben da aka yi ya kawo ma yakin neman zabensa tangarda.
A wani hannun kuma dan takarar jam’iyyar PDP a zaben jihar Edo Fasto Osagie Ize-Iyamu ya soki lamarin daga ranar zaben da aka yi zuwa 28 ga watan satumba. Ya kara da cewa dalilan da hukumar zaben ta kasa (INEC) ta bayar a matsayin hujjanta na daga zaben ba masu kwari bane, inda yace INEC bata tuntubesu ba kafin ta yanke hukuncin dagawa.
The post Zan samar da wuta mai karfin 450mw a Edo – Obaseki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us