A Cire Kwamitin Gaggawa Na Kayan Gwamnatin Tarrayya A Legas – Ambode
Gwamna Ambode na Jihar Legas yayi kira ga gwamnatin tarayya data cire kwamitin gaggayawa mai kula da gine ginen gwamnatin tarayya dake a Legas.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta hanyar mai taimaka mashi akan hudda da jama’a Habib Aruna a ranar Talata 11 ga watan Agusta.
Gwamnan ya zargi kwatin na gaggawa da yunkurin Danne hakkin Jihar ta Legas. Wannan korafin da gwamnan yayi yazo bayan korafe korafe da ake tayi aka kwamitin cewa yana wuce gona da iri.
Ambode yace: “Wannan kwamitin na gaggaywa na gwamnatin tarayya har yanzu ana ta kokwantan iko kafa shi. Suna zuwa suna amshe gidaje suna kulle gine gine mallakin gwamnatin tarayya dana Jihar. Kwamitin na cigaba da yin hakan duk da kuwa cewa suna sane da cewa, babbar Kotun dake a Legas ta dakatar dasu daga yin haka, kuma an buga wannan umurnin na kotun manyan Jaridun kasar nan.”
Gwamna Ambode yayi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari daya ruguza kwamitin daga wannan aikin da sukayi. “Domin abunda sukeyi na wasa da tsoron Jihar Legas.”
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.The post A Cire Kwamitin Gaggawa Na Kayan Gwamnatin Tarrayya A Legas – Ambode appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us