Nasarorin Da Buhari Ya Samu A Cikin Watanni 2 – Hakeem
Malam Oladele Hakeem, Edita a Naij.com yayi rubutu akan nasarorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a cikin watanni 2 bayan da aka rantsar da shi.
Manyan nasarorin daya samu sun hada da;
1. Samun wutar lantarki: Ada can, wutar lantarki labari ce a Najeriya. Lokutta kadan ne ake samun wutar lantarki.
Amma kimanin watanni biyu da suka wuce, wuta ta fara dai dai ta. Wannan kuma nada nasaba ne da kulawar shugaba Buhari.
2. Azama wajen yakar Boko Haram: Daga hawan shugaba Buhari, kasashen duniya suna ta nuna niyyar su wajen taimakam Najeriya ta yaki Boko Haram. Amurka, Britaniya da sauran kasashe duniya duk sun bayyana niyyar su wajen taimakawa a yaki Boko Hara.
3. Zuwan Buhari Amurka: Zuwan da shugaba Buhari yayi Amurka ya jawo ma Najeriya alherai da yawa. Cikin su hadda Dala Biliyan 2.1 wanda Bankin duniya ya ba Arewa maso Gabacin Najeriya.
4. Aikin gyran Ogoni (HYPREP): Shugaba Buhari ya amince da nada kwamitin gudanarwa na Hydrocarbon Pollution Restoration Project. Wanna ya nuna cewa shugaba Buhari shugaba ne mai adalci kuma baya nuna bangaranci.
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.
The post Nasarorin Da Buhari Ya Samu A Cikin Watanni 2 – Hakeem appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us