Sports Betting

Trending

random

Shin Mutanen Jonathan Sun Fara Maido Da Abubuwan Gwamnati?

Wani bincike da jaridar Leadership ta gudanar ya nuna cewa wasu jami’an gwamnatin Jonathan sun fara maido da abubuwan gwamnati dake a hannun su.

Binciken ya nuna cewa sun fara maido da Janareta, kujeru, gidaje da kuma motoci. Wata majiya daga fadar shugaban kasa wadda bata so a bayyana sunan ta ta bayyana cewa tun ranar Litinin 17 ga watan suka fara kira suna bayyana abubuwan dake hannun su wanda yan uwan su suka dauka.

Majiyar tace duk da kokarin da sukayi domin su maido da abubuwan, dole ne suyi bayani sosai kafin a bincike su.

Tace:  ”Tun yau (Jiya) suke ta kira suna bayyana cewa suna sane da cewa ‘yan uwan su na zanne a gidajen gwamnati alhali su suna kauyukan su ko kuma kasashen wajen. Amma wannan kaddara ta riga fata ce, domin kuwa sai an bincike su. Don shugaban kasa ran hi yaa baci sosai.”

Da aka tambayi majiyar ko suna da sunayen wadan suka kira wayar tace: “Eh muna da sunayen su a hannu. Abunda nukeyi a yanzu shine bincikewa domin mu gano shin sun saye su ne akan tsari kamar yadda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fara ko kuwa. abunda bincike ya nuna dashi zamuyi amfani.”

Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.

The post Shin Mutanen Jonathan Sun Fara Maido Da Abubuwan Gwamnati? appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


Shin Mutanen Jonathan Sun Fara Maido Da Abubuwan Gwamnati? Reviewed by Olusola Bodunde on 04:26 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.