Sports Betting

Trending

random

An Kama Mutum Guda 4 Akan Damfarar Gwamnatin Tarayya

Hukumar hana almundahana, ta gurfanar da mutum guda 4 a gaba Babbar Kotun Tarayya a Abuja akan damfarar gwamnatin tarayya Naira Biliyan 1.2.

Jaridar PM ta ruwaito cewa wandanda aka gurfanar a ranar Talata 15, ga watan Satumba a gaba Mai Shari’a Abubakar Talba akan laifuka na hadin kai da karban kudi da karya.

Rahoton ya nuna cewa mutum guda 4 da sunayen su, Ibrahim Ahmed Mazangari, Muhammed Sani Sulaiman, Hajia Fatima Mazangari da Saleh Yerima, sun sa sunayen su acikin fansho lokacin da aka basu kwangilar duba sunayen yan fenshon.

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Tarayya, Steve Orosanye shine ya bayar da kwangila akan duba hanyoyin da za’a rage almundahanar dake cikin fanshon. Amma su sun dauki damar kwangilan sun saka sunayen su.

Domin Fatimah Mazangari bata gurfana ba, Mai Shari’a bai yardarm masu da su amince da laifin su ba domin ayi masu sassauci.

Mai shari’ar Talba ya basu beli na tsarba kudin Naira Miliyan 10. Zai cigaba da sauraron karar a Nuwamba 2 da 3, 2015. An umurci wadanda ake zargi su zauna a kurkuku.

Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.

The post An Kama Mutum Guda 4 Akan Damfarar Gwamnatin Tarayya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


An Kama Mutum Guda 4 Akan Damfarar Gwamnatin Tarayya Reviewed by Olusola Bodunde on 01:56 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.