Sports Betting

Trending

random

Manyan Labarai Guda 10 Wadanda Suka Yi Fice A ranar Litinin

Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda suka yi fice a ranar Litinin 28 ga watan Satumba. Ku duba domin ku same su.

Muhammadu Buhari, President of the Federal Republic of Nigeria, speaks the United Nations Sustainable Development Summit to the at the United Nations General Assembly im New York September 25, 2015. AFP PHOTO / TIMOTHY A. CLARY (Photo credit should read TIMOTHY A. CLARY/AFP/Getty Images)

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a majalisar dinkin duniya a New York babban birnin kasar Amurka

1. An bata ma shugaba Buhari tsarin zuwan shi New York, Amurka.
Rahotanin sun nuna cewa, Babbar ambasadar Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Farfesa Joy Ogwu ta bata ma Shugaba Buhari tsarin zuwan shi Amurka.
2. Majalisar Dattawa na shirin amsar sunayen Ministocin Buhari.
Majalisar Dattawan Najeriya na jiran amsar sunayen Ministocin Buhari. Hakan na ika kaiwa har zuwa ranar Laraba kamar yadda ake tsammani.
3. Yan Boko Haram sun kai hari, sun kashe mutane 20.
Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a Malari da kuma kauyukan Konduga inda suka kashe kimanin mutane 20 a wadannan wajajen.
4. Yadda wani dan Najeriya ya tsira daga cinkoson Makkah.
Wani Mahajjacin Najeriya dag Jihar Kano, Hamza Musa kabir ya bayyana ma wakilin AFP na Kano, Aminu Abubakar yadda Allah ya cice shi da ba’a tattake shi ba a Mina, Makkah.
5. Wani tsohon Gwamna ya bukaci yan Arewa suyi Allah wadai da nade naden Buhari.
Balarabe Musa, tshon Gwamnan Kaduna ya bukaci yan Arewa suyi Allah wadai da nade naden da shugaba Buhari yayi kawo yanzu. Inda yace hakan ya saba ma adalcin rayuwa.
6. Olu Falae ya bayyana dalilin daya sanya aka sace shi.
Cif Olu Falae ya bayyana dalilin daya sanya wasu Makiyaya suka sace shi. Sannan kuma ya bayyana cewa Yan Sanda basuyi wani abu domin sakin shi, inda ya  bayyana cewa iyalin shi sun biya makudan kudi domin a sake shi.
7. Wasu Sanatoci na tsoran shugabantar wasu kwamitoci saboda Buhari.
Wasu Sanatoci masu goyan bayan Saraki sunki yadda su shugabanci wasu kwamitoci a cikin majalisar Dattawa saboda suna tsoran Buhari ya bincike su.
8.  Fayose ya roki Buhari ya saki kudin Jihar Ekiti.
Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya roki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari daya ida sakin kudin gudunmuwa da aka fara ba jihar.
9. Wamakko ya maganta akan shari’ar saraki
Sanata Aliyu Wamakko (Sakwatto), ya maganta akan shari’ar da hukumar CCB take yi ma Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki.
10.  Shugaban Jam’iyyar APC ya kira taron gaggawa.
Shugaban Jam’iyyar APC, John Odigie – Oyegun,  ya kira wani taron gaggawa na kwamitin gudanarwa na Kasa domin tattaunawa akan sunayen Ministoci da ake tsammanin shugaban Kasa Muhammadu Buhari zaya tura ma Majalisar Dattawa domin tantancewa.
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.

The post Manyan Labarai Guda 10 Wadanda Suka Yi Fice A ranar Litinin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


Manyan Labarai Guda 10 Wadanda Suka Yi Fice A ranar Litinin Reviewed by Olusola Bodunde on 03:12 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.