EFCC Ta Kama Wani Tsohon Gwamnan Jam’iyyar PDP
Bayar da rahoton, kwamishin na hana almudahana (Economic and Financial Crimes Commission) ta kama wani tsohon gwamnan jihar Kebbi, Usman Saidu Dakingari akan zargin cin hanci da rashawar Naira Biliyan 3.8 daga jihar.
Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito wanda an tsare wani tsohon gwamnan a yau Litinin 19, ga watan Oktoba a daidai karfe 10 da safe. A halin yanzu, masu binciken EFCC suna tantancewar shi.
Idan baza ku manta ba, an zabe Dakingari na gwamnan jihar Kebbi akan dandamalin jam’iyyar Peoples Democratic Party a 2007.
Shine yayi aure da yar tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa Yar’Adua.
Kwanan nan, kwamishin na hana almudahana ta kama matar Dakingari, Zainab. An zargi da ta kan cin hanci da rashawar Naira Biliyan 2 na mijinta inda shi yake gwamnan jihar Kebbi.
A sati da ya wuce, kwamishin na hana almudahana ta gayyata tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Cif Godswill Akpabio akan tambayoyi. An kira ga shi akan cin hanci da rashawar Naira Biliyan 108 daga aljuhun jihar. Amma bayan haka, an saki da shi.
The post EFCC Ta Kama Wani Tsohon Gwamnan Jam’iyyar PDP appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us