Kada Daliban Soja Su Kara Sanya Kayan Mu – Hukumar Soji
Hukumar Sojin Kasa ta hana tsofaffin daliban Soja na makarantar Daliban Soja dake Zariya sanya kayan Soja ko kuma abubuwan su.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa kayan da tsoffafin daliban soja ke sakawa na bata sunan Sojoji kuma yana wasan da tsaron al’umma.
Jawabin daga Kanar Sani Kukasheka, Daraktan Labarai na sojin Kasa ya bayyana cewa sanya kayan Soja ga wanda ba Soja ba haramun ne. Yace: “Da yawa cikin yaran sun bar soja amma suna rike da kayan soja. Muna kara jadda cewa sanya kayan Sojoji ga wanda ba Soja ba haramun ne.
“Mafi yawancin masu sanya kayan nan toffin aliban makarantar soja ne wadanda suka bar makaranta amma suna rike da kayan soja.
“Duka tsofaffin daliban da suka bar makaranta daga 2012 muna tsammanin su kawao kayan su da sauran abubuwan soja dake hannun su. Domin yin amfani da kayan soja haramun ne.
“Sanya kayan sojoji laifi ne wanda keda hukunci a karkashin dokar Criminal Code, sakin layi na 109, 110, da 251. Muna aiki tare da sauran hukumomi domin kama wadanda ke yin haka a manyan makaratun gaba da sakandare.”
The post Kada Daliban Soja Su Kara Sanya Kayan Mu – Hukumar Soji appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
Kada Daliban Soja Su Kara Sanya Kayan Mu – Hukumar Soji
Reviewed by Olusola Bodunde
on
04:24
Rating:
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us