Sports Betting

Trending

random

SABON LABARI: Dan Takarar Jam’iyyar PDP A Zaben Gwamna Ya Mutu

Sabon labari tana fitowa ta bayyana cewa Sanata Gyang Nyam Pwajok, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Filato a Asabar 11, ga watan Afirilu ya rasu.

Senator Pwajok

Sanata Gyang Pwajok, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Filato

Jami’i mai hudda da jama’a na jam’iyyar Peoples Democratic Party, Olisa Metuh, shine ya gaya ma jaridar Sahara Reporters.

A kwanan nan, Sanata Pwajok ya fadi karar shi da gwamnan jihar Filato, Simon Lalong a gaba kotun zabe. Lalong ne dan takarar All Progressives Congress a zaben gwamnan.

Wani labari daga iyalin Sanata Pwajok, ya bayyana wanda ya mutu saboda ciwon koda a kasar Indiya. Amma a halin yanzu, jaridar Naij.com ba ta tabbatar da mutuwan shi ba.

A wannan shekara da wuri, Sanata Pwajok ya musanta jita-jita da ya mutu.

An haifaffe da shi a watan Maris 15, 1966 a Jos, birnin jihar Filato. Ana kira Gyang Nyam Shom Pwajok da sunan “GNS.” Yayi yaron shi a Jos.

Ya tafi makarantan faramaren Jos Township (1972 – 1977), makarantan Saint Murumba, Jos (1977 – 1982), makarantan Preliminary Studies, Keffi (1982 – 1984), Jami’ar Ahmadu Bello Zaria (1984 – 1987). Ya samu Digiri Masters a tattalin arziki, siyasa da ilimin cigaba a 1991 a Jami’ar Jos, inda shi mai shekaru 24.

The post SABON LABARI: Dan Takarar Jam’iyyar PDP A Zaben Gwamna Ya Mutu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


SABON LABARI: Dan Takarar Jam’iyyar PDP A Zaben Gwamna Ya Mutu Reviewed by Olusola Bodunde on 07:51 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.