Buhari Ya Nisanta Kanshi Daga Dokar Shafukan Sada Zumunta
Shugaba Muhammadu Buhari ya nisanta kanshi daga dokar da yan majalisa ke kokarin yi wadda zata hukunta masuyin amfani da shafukan sada zumunta suna zagin jami’an gwamnati.
Wannan ya fito me Daga bakin babban Mai taimaka ma shugaban kasa ta harkar hudda da jama’a, Garba Shehu. Shugaba Buhari yace:
“Ni an rantsar dani ne domin in kare kundun tsarin mulkin Najeriya. Bazani sanya ma Wata doka wadda ta saba mashi hannu ba.
“Damar bayyana raayi wani abu ne wanda duka Duniya ta yadda dashi domin shugabanni su san halin da talakawa suke ciki.”
Shugaba Buhari ya tabbatar ma mutane da cewa majalisar Najeriya majalisar Damakaradiyya ce. Ya tabbatar zasuyi abunda ya kamata.
Kudurin dai Sanata Na’Allah ne ya kawo shi. Kudurin idan ya zama doka zaya zaman sanadin daure mutane masu baza karya ko kuma suna zagin shugabanni.
Kudurin ya samu karantawa na biyu, amma kafin ya zama doka, za’ayi zama domin aji ra’ayin Mutane. Ikon bayyana raayi Wata dama ce wadda kasashe da yawa na duniya suka amince da Ita. Tana ba Yan kasa dama Su bayyana ra’ayin su kuma su sanar da sauran yan’uwan su abunda ake ciki.
The post Buhari Ya Nisanta Kanshi Daga Dokar Shafukan Sada Zumunta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us