Manyan Labarai Guda 10 Wadanda Sukayi Fice A Ranar Litinin
Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda Sukayi Fice a ranar Litinin 7 ga watan Disamba. Ku duba domin samun su.
1. Zaben Bayelsa: Babu Wanda Ya Lashe Zaben – Hukumar Zabe
Hukumar zabe ta kasa ta bayyana cewa babu wanda ya lashe zaben Bayelsa wanda aka gudanar a ranar 5 ga watan Disamaba.
2. In Ku Kaka Kashe Mani Soja Sai Na Kashe Ku Duka – Kalu
Tsohon gwamna Orji Kalu ya shawarci gwamnatin tarayya ta kashe duka masu zanga zangar Biafra idan suka kashe Soja daya.
3. Naga Mutuwar Audu, Buhari Kuma Zaya Kashe Kiristoci – Fasto
Wani dan karamin Fasto mai suna Johnson Suleiman dake jihar Edo ya bayyana cewa hana zuwan mutuwar Audu.
4. Yadda Gwamnatin Jonathan Ta Kasance – Babangida
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Ibrahim Babangida, ya bayyana wasu abubuwa akan gwamnatin Jonathan.
5. Kotu Ta Kara Korar Wata Sanata Ta PDP
Kotu ta soke zaben Sanata Misis Uche Ekwunife dake daga jihar Enugu.
6. Zaben Kudancin Bayelsa Ya Haddasa Rigima
Manyan Jam’iyyun APC da PDP suna kokarin ganin samun kuri’un mutanen kudancin Bayelsa. Hakan ya jaza fitina sosai.
7. PDP Ya Gamsu Da Soke Zaben Kudancin Bayelsa
Jam’iyyar PDP tayi jinjina ga mutanen kudancin Bayelsa akan yadda “suka hana APC yin magudi” kamar yadda Jam’iyyar ta bayyana.
8. Wasu Yan Bayelsa Sunyi Zanga Zanga A Wajen Tattara Kuri’u
Wasu Mutanen Bayelsa sunyi zanga zanga a inda ake tattara kuri’u.
9. Shugaba Buhari, Atiku, Sun Halarci Taron Wallafa Littafin Minista Onu
Shugaban kasa Munammadu Buhar, tara da Atiku Abubakar sun halarci taron fitar da littafi wanda Minista Kimiyya Ogbonnaya Onu yayi a dakin taro na kasa da kasa na Umar Musa Yar’adua.
10. Yan Ta’adda Sun Kaima Mukaddashin Ciyaman Din PDP Na Bayelsa Hari
Wasu Yan ta’adda sun kaima mukaddashin Ciyaman na PDP na JIhar Bayelsa a ranar 4 ga watan Disamba.
The post Manyan Labarai Guda 10 Wadanda Sukayi Fice A Ranar Litinin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us