Manyan Labarai Guda 10 Wadanda Sukayi Fice A Ranar Litinin
Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Litinin 11 ga watan Janairu. Ku duba domin ku same su.
1. Ana Murna A Bayelsa Domin Dickson Ya Lashe Zabe
Magoya bayan PDP sunyi zagayen gari a jiya a yayin da hukumar zabe ta tabbatar da cin zaben Dickson.
2. Metuh Yayi Wani Bayani Mai Tsoratarwa
Olisa Metuh ya fada ma EFCC cewa ya amshi kufi daga hannun Sambo Dasuki. Sannan kuma yayi wani bayani mai ban tsoro.
3. EFCC Ta Kama Shugaban Hukumar NBC
Hukumar EFCC ta kama Emeka Mba, shugaban hukumar EFCC a yayin da ake zargin shi da almundahana da Naira Biliyan 15.
4. An Sace Dan Takarar Jam’iyyar APC
An sace dan takarar jam’iyyar APC na jihar Ondo a yayin da yake kan hanyar Akure daga Abuja.
5. Abunda Ya Sanya Bamu Kama Jonathan Ba
Hukumar EFCC tayi bayani akan dalilin daya sanya har yanxu bata kama tsohon shugaban kasa Jonathan ba.
6. Asari Dokubu, Fashehun Zasu Ziyarci Owerri
Shugabannin kungiyoyin NDPVF, da kuma OPC zasu shiyarci jihar Owerri kafin a gudanar da zaben Biafra.
7. Fasto Adeboye Zaya Mutu
Karants kaji abunda Fasto adeboye ya gaya ma matar shi.
8. Ba Zani Maido Da Haramtattun Kudaden Da Aka Babi Ba – Olu Falae
Shugaban jam’iyyar SDP, Cif Olu Falae ya bayyana cewa ba zaya maido da haramtattun kudaden da aka bashi ba.
9. Jam’iyyar APC Ta Hana Prince Audu, Obi Shiga Jam’iyyar
Jam’iyyar APC ta hana attajirin mai kufi Prince Adu Eze da kuma tsohon gwamnan Anambara Peter Obi shiga jam’iyyar.
10. Messi Yaci Kambin FIFA Na 2015
Jarumin dan wasannan Lionel Messi, ya sake cin kambin Kungiyar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) watau Ballan D’or 2015.
The post Manyan Labarai Guda 10 Wadanda Sukayi Fice A Ranar Litinin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us