Buhari ya isa Malabo, babban birnin kasar Equatorial Guinea
– Shugaban kasan Najeriya ya isa Malabo, Equatorial Guinea
– Shugaban ya samu tarba daga shugaba Nguema
– Zasu tattauna akan sha’anin tsaro
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu isa babban birnin Equatorial Guinea, Malabo, inda zaya kwanaki 2.
KU KARNTA: Buhari ya nada Mrs Adejoke amai bashi shawara
Shugaban ya samu tarba daga shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo a filin jirgin sama na Malabo. Shugaban kasa ya tafi kasar Equatorial Guinea tare da Ministan harkokin kasashen waje, Hajiya Khadija Ibrahim, Gwamnan Jihar Kogi, Babagana Munguno, mai bashi shawara kan sha’anin tsaro.
Shugabannin 2 zasu tattauna akan tsaro na yankin Nija Delta da kare dukiyar wajen, sannan kuma zasu tattauna akan kare kasashen 2 daga da ta’addanci, satar fahimta, satar mai, satar mutane da dai sauran su.
KU KARANTA: Buhari ya jajanta mutuwar Ocholi
Shugaba Buhari na gaisawa da mutane
Ana sa ran jibi shugaban Kasa zaya dawo. Wannan dai itace fita ta sama da dozin da shugaba Buhari yayi tun hawan shi mulki a matsayin shugaban Najeriya. Ana sa ran kuma zaya tafi Amurka idan ya dawo bayan kwana kada. Zaya tafi Amurka inda zaya shiga tattaunawa da sauran shugabanni da kuma kungiyoyi na duniya akan makamashin Uranium wanda ake hada makamin Nuclear dashi.
The post Buhari ya isa Malabo, babban birnin kasar Equatorial Guinea appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us