Buhari ya nada sabon shugaban SMEDAN
– Buhari ya nada sabon shugaban SMEDAN
– Ummaru Dikko Radda ne sabon shugaban
– Radda shine shugabann ma’aikatan gwamnan jihar Katsina
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dakta Ummaru Dikko Radda a matsayin sabon shugaban hukumar SMEDAN.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya tafi Malabo
Wani jawabi wanda fito a ranar 14 ga watan Maris daga B olaji Adebiyi, jami’i mai hudda da jama’a na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, ya bayyana cewa nadin zaya fara ne daga yau ranar da akayi nadin.
Kafin shugaba Buhari ya nada Radda, Radda shine shugaban ma’aikatan gwamnan Jihar Katsina. Alhaji Aminu Bello Masari.
Radda wandan tsohon malamin makaranta ne, ma’aikacin Banki, kuma shugaban karamanar hukuma, yana da Digiri akan tattalin arziki na bunkasa Noma a 1996 daga jami’ar Tafawa balewa dake a Bauchi.
KU KARANTA: Matasa sun nemi Buhari ya basu N5000
Daga tsakanin 1998 zuwa 2015, ya samu Digiri na 2 akan tattalin arziki na bunkasa Noma, Digiri na 2 akan Diflomasiyya sannan kuma ya zama Dakta akan tattalin arziki na bunkasa Noma.
Ummaru Dikko Radda gogagge ne wajen aiki kuma ya nuna kwarewa a wuraren da ya rike dabam dabam. Anan sa ran zaya cigaba da aiki kamar yadda ake tsammani daga gare shi.
The post Buhari ya nada sabon shugaban SMEDAN appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us