Gwamnatin Buhari ta bude shiri domin matasa
– Gwamnatin shugaba Buhari ta bude wani sabon shiri mai suna Youth Enterprenuership Support (YES)
– A yau ne aka bude sabon shirin
– Za’a samar ma matasa 36,000 da aiki
Domin samar ma matasa aiyukan yi kamar yadda akayi masu alkawari, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bude wani sabon shiri daga (BoI) mai suna YES. An bude shirin ne a yau a Abuja.
KU KARANTA: Ya kamata Buhari ya tattauna da masu neman Biafra – Anohu
A cewar Okechukwu Enelamah, karamin Ministan ciniki da kasuwanci, wanna na daga cikin shirin da gwamnatin tarayya tayi domin ta sama ma matasa 36,000 da aiyukan yi a cikin alkawarin samar da aiyuka Miliyan 3.5 da tayi alkawari cikin shekaru 3.
Masu neman a basu aron kudin zasu bada kwalin NYSC din su, kona makarantar su a matsayin jingina domin a basu kudaden. Sannan zasu kawo mutane 2 a matsayin iyayen gida.
Mai neman kudaden zasu iya samun aron kudade har Miliyan 10 wanda za’a biya cikin shekaru 3 zuwa 5. Sannan kudin riba za’a bia shi cikin lamba daya.
Waheed Olagunju, wanda shine shugaban Bankin BoI, ya bayyana cewa a yanzu suna aiki da kwarrarun kamfanoni 40 a fadin Najeriya domin ganin an fara shiri na farko. Ya bayyana cewa kimanin wadanda sukayi karatun makarantar gaba da Sakandare 40 basu da aiyukan yi. Sannan akalla mutane Miliyan 8 ke shiga neman aiyuka a kowace shekara.
The post Gwamnatin Buhari ta bude shiri domin matasa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us