Sports Betting

Trending

random

Saraki ya sha alwashin gyara asibitin majalisa

 

– Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ziyarci asibitin majalisa dake a Area 11, Abuja

– Ya sha alwashin gyara asibitin yafi kowanne a Najeriya

– An kafa asibitin ne a 2009

Sanata Bukola Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya sha alwashin gayara asibitin yan majalisar Najeriya dake a Area 11 dake a babban birnin tarrayyar Najeriya, Abuja. Ya je ne a jiya Litinin 14 ga watan Maris.

A wani jawabi da Bamikole Omishore, mai taimaka ma shugaban majalisa akan sababbin hanyoyin yada labarai, ya bayyana cewa shugaban majalisar ya sha alwashin gyara asibitin domin ya kula da yan majalisa da kuma ma’a’ikatan majalisa duka kimanin 6000.

Ya bayyana cewa muradin asibitin shine ya habbaka ya kula da yan majalisa da kuma mutanen gari wanda hakan zaya habbaka zumunci tsakanin mutane da yan majalisar.

Shugaban Majalisar kuma ya gana da shugaban sibitin, Dakta Hamza Bashiru, Daraktan aiyuka Dakta Eme Moma-Efretuei, babban sakatare da kuma sauran ma’aikata inda ya bayyana cewa ya kamata a gyara asibitin.

Asibitin an kafa shine a 2009 domin ya kula da lafiyar Yan majalisar wakilai da dattawa, iyalan su, ma’aikatan su da kuma duk wanda ya ziyarci majalisar.

Gudan asibitin majalisar nada Gadaje 20, Gadaj 100 na kwantar da marassa lafiya, sashen duba hakora, sashen fida da sashen kula da lafiya na gaggawa.

Shugaban Majalisa Saraki, ya zagaya asibitin inda ya gana da ma’aikata wadanda suka bayyana cewa asibitin yana bukatar gyara.

Ma’aikatan sun bayyana cewa asibitin yana zaune ne a gida da ake haya. Sun nemi taimakon majalisa ta 8 domin a kammala ginin wuuein asibitin na din din din dake yankin Gudun a Abuja.

Shugaban Majalisa, Bukola Saraki, wanda shi kanshi Likita ne ya sha alwashin cewa zaya gyara asibitin kuma ma’aikatan zasu ga canji.

The post Saraki ya sha alwashin gyara asibitin majalisa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


Saraki ya sha alwashin gyara asibitin majalisa Reviewed by Olusola Bodunde on 10:36 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.