Yan sanda na neman taimakon Ubangiji – Sifeto Janar
– Sifeto Janar na yan sanda ya bayyana cewa yan sanda na neman taimakon Ubangiji domin suyi aiki
– Ya bayyana haka a ranar Lahadi lokacin taron wasannin yan sanda karo na 11
– Ya nemi jami’an shi su ringa addu’a sosai
Sifeto janar na yan sanda a lokacin taron
Sifeto Janar na yan sanda ya bayyana cewa yan sanda na neman taimakon ubangiji domin suyi aikin su yadda ya kamata.
KU KARANTA: Bola Tinubu ya caccaki karamin Ministan Mai
Ya bayyana haka ne a Abuja a Cibiyar kirista ta kasa, a ranar Lahadi 27 ga watan Maris lokacin addu’o’i domin buda wasa karo na 11 wanda yan sanda ke gudanarwa.
Yace ” Karin neman imani da ubangiji yana da amfani ga dan sanda domin ubangiji ne ke sanya ikonnsa a cikin mu, duk da cewa aikin mu yana da wahala, domin mu kare mutanen kasa.
” Idan kai ma’aikacin banki ne, idan kayi kuskure asarar kudade za’ayi. Amma dan sanda idan yayi kuskure rai za’ayi asara. Muna bukatar Ubangiji a tare damu domin kada mu tura mutanenn mu inda ran su zaya salwanta.
a wani labarin kuma, shugabar WARDC ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari daya duba yanda yan sanda suka sayi karnuka har na Naira Miliyan 600.
Ms Ketefe ta bayyana cewa hakan da yan sanda sukayi ya saba ma tsarin kasa na duna cikin gida domin saye-saye na lokacin tsanin tattalin arziki a kasa.
The post Yan sanda na neman taimakon Ubangiji – Sifeto Janar appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us