Sports Betting

Trending

random

Amurka ta gano inda yan matan Chibok suke

– Kasar Amurka ta bayyana inda inda yan matan Chibok suke

– Ta sha alwashin taimaka ma Najeriya

– Ta nemi yayen yan matan dasu kara hakuri

Amurka

Shugaba Buhari ater da shugaba Obama na Amurka

Jami’an gwamnatin kasar Amurka sun bayyana cewa su tare da gwamnatocin wasu kasashen Afirika sun gano inda wasu tarin yan matan Chibok da aka sace shekara 2 da suka wuce suke.

KU KARANTA: PFN ta maganata akan dokar wa’azi ta El-Rufai
Amurka bayyana cewa basuyi kokarin ceto yan matan bane saboda idan akayi yunkurin yin hakan yan ta’addan zasu iya kashe ya matan ko kuma su farma al’ummar dake kusa dasu da kauyuka.

Sun bayyana cewa anyi amfani ne da labarai da ake hada a a kasashen da abun  ya shafa inda akayi amfani da jirgi mai Kemara aka dauki hotunan inda yan matan suke.

Jami’an Amurka kuma sun bayyana cewa abun takaici yadda wasu mata masu tarin yawa yan Boko Haram keyi masu fyade inda wasu ake tilasta masu aure ko kuma ma a kashe su.

Janar Rodriguez yace ”  An kai yan matan wani kebebben wuri inda yake a nesa. Baza mu iya cewa ga wurin a inda yake ba.

” Matsalar anan shine, ta yaya zaka iya gane inda mutane da yawa suke kuma a wurare daban daban? Wannan yafi karfin jami’an cikin gida na wadannan kasashen.

Idan za’a iya tunawa, kimanin shekara 2 ke na da sace yan matan Chibok daga makarantar Sakandare dake a garin Chibok a cikin jihar Borno. A ranar14 data wuce ne aka gudanar da bikin tunawa dasu a Unity Fountain dake a birnin Abuja

 

The post Amurka ta gano inda yan matan Chibok suke appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


Amurka ta gano inda yan matan Chibok suke Reviewed by Olusola Bodunde on 13:55 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.