Kungiyar IPOB na cikin rudani akan matsayin Kanu
– Dacta Dozie Ikedife, tsohon shugaban kungiyar Ohanaze Ndigbo, ya bayyana cewa Nnamdi Kanu bashi bane shugaban IPOB
– Ya bayyana cewa Nnamdi Kanu shugaban kungiyar Rediyon Biafra ne, kawai dai yayi amfani da sunan IPOB ne
– Jami’i mai hudda da jama’a na IPOB, Emma Powerful, ya musanta zancen
Mutanen kungiyar IPOB sun rikice akan wanene shugaban kungiyar, Jaridar The Sun ta ruwaito labarin.
Wanna yazo bayan da Dakta Dozie Ikedife, tsohon shugaban kungiyar Ohanaze Ndigbo ya bayyana cewa bashi ya kirkiri IPOB ba kuma ba shi bane shugaban kungiyar.
Ya bayyana cewa Kanu shine shugaban Rediyon Biafra, amma ba shi bane shugaban kungiyar IPOB domin satar suna yayi.
Ikedife ya bayyana cewa sune shugabannin kungiyar kuma su suka kafa ta domin ta zama zauren koli na tafiyar da harkokin yan Biafra da kare hakkin bil adama.
Emma inda Emma Powerful yayi saurin magantawa, yayi Allah wadai da ikirarin Ikedife da kula da yake yi wajen kare hakkin bil adama.
Yace “Wasu labarai a shafukan jarida masu cewa Nnamdi Kanu bashi bane shugaban kungiyar IPOB ba gaskiya bane.
” Kungiyar Bilie, watau Biafra liberation in Exile an kafa tane da jimawa, sai daga baya ne Nnamdi Kanu ya nada Ikedife da sauran wasu manyan a zauren koli na IPOB domin su ringa bada shawarwari kawai.
Hukumar DSS ta kama Nnamdi Kanu ne a watan Aktoba na shekarar data wuce inda yanzu yake tsaye yana fuskantar zargi akan laifuka 10 wadanda suka hada da kokarin juye gwamnati.
Sama da mutane 30 suka mutu tun fara zanga-zangar a saki Nnamdi Kanu a jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya.
The post Kungiyar IPOB na cikin rudani akan matsayin Kanu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us