Sports Betting

Trending

random

Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Talata

Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Talata 19 ga watan Afrillu na 2016. Ku duba domin ku samu wadannan manyan labaran.

13055409_999846140107726_8096275071292581493_n

1. Hukumar EFCC ta kama maitamaka ma tsohon shugaban kasa Jonathan a Legas

A jiya ne hukumar EFCC ta kama daya daga cikin manyan yaran stohon shugaban kasa Jonathan, watau Waripamowei Dudafa akan zargin cin hanci na daligat wanda ya kai darajar Naira Biliyan 10.

2. Yan Boko Haram sun kaima sojojin Najeriya hari a Kareto

A jiya ne sojojin Najeriya suka samu kansu karkashin hari daga yan Boko Haram a Kareto,

3. Jam’iyyar PDP ta zargi Diyar shugaba Buhari da hawan jirki babban aji zuwa Ingila

Jam’iyyar PDP tayi ikirarin cewa daya daga cikin ya’yan shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hau jirgi babban aji zuwa kasar Ingila.

4. Saraki ya jagoranci zaman majalisa ajiya duk da tugumar shi da akeyi a kotu

Shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bude taron zaman majalisa a jiya inda ya hannanta shugabancin zaman zuwa ga mataimakin shugaban majalisa, Ike Ekweremadu.

5. Alkalin mai shari’ar Saraki yayi latti a jiya

Alkali mai shari’ar shugaban majalisa yazo kotu latti a jiya inda yazo bayan awa 1.

6. Ameachi ya bayyana cewa akwai manyan matsaloli a tare da Buhari

Ministan Sufuri ya bayyana cewa shugaba Buhari ya fara gazawa wajen cika alkawurran da yayi ma mutanen Najeriya. Ya kuma bayyana cewa akwai manyan mutane guda 8 wadanda zasu iya lalata gwamnatin tashi.

7. Shugaba Buhari ya gana da Osinbajo, Udo Udo Udoma akan kasafin kudin 2016

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saken ganawa da Ministan shirye shiye inda suka tattauna akan kasafin kudi.

8. Zuwa kotun CCT: Yan Najeriya suniy Allah wadai da Sanatoci

Wasu yan Najeriya sunyi Allah wadai da Santocin dake barin aikin su suna zuwa rakijiyar Bukola Saraki kotu

9. Wata mata tayi fada da wani saurayi a tsirara

Bayan da fada ya kacame, wata mata bata hakura da fadan da take yi da wani saurayi ba har sai da takai tayi tsirara.

10. An kama wata matar aure tana lalata da wani saurayi

Wata matar aure da wani saurayi sun leki a jikin juna a yayin da suke aikata masha’a a garin Benin.

 

The post Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Talata appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Talata Reviewed by Olusola Bodunde on 23:46 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.