Sports Betting

Trending

random

Shugaba Buhari zaya ziyarci kasar China

– Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zaya tafi kasar China ziyara a ranar Lahida

– Shugabanasa zayayi kwanaki 4 a kkasar

– Zaya tattauna da shugaban kasar China akan tattalina arziki da sauran lamurra

Buhari

Shugaban kasa Buhari

Femi Adesina, jami’i mai hudda da jama’a na shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zaya tafi kasar China ziyarar kwanaki 4 inda zasu tattauna da shugaba Xi Jinping na kasar China.

Shugaba Buhari zai shine shugaban kasar Africa na farko wanda shugaban kasa China, Xi Jinping ya gayyata domin yaje a tattauna dashi.

Shuagban kasa Buhari zaya samu rakiya daga Ministocin; Ruwa, Sufuri, Abuja, Noma, harkokin kasashen waje, kasuwanci, Wutar lantarki, gidaje da aiyuka.

Tawagar gwamnatocin 2 zasu tattauna ne akan yadda China zata iya taimakama cigaban Najeriya.

Femi Adesina ya rubuta ” Shugaban kasa Muhammadu Buhari zaya tafi kasar China na tsawon kwanaki 4 inda zasu tattauana domin neman taimakon Beijing akan cigaban Najeriya ta wuraren, Sufuri, wutar lantarki, ruwan sha, noma, da kuma gidaje.

Manyan ma’aikatun kasashen guda 2 zasu tattauna akan yadda za’a habbaka kasuwanci da kuma dangantaka dake tsakanin kasashen guda 2.

Shugaba Buhari da tawagar shi zasu kuma ziyarci Shanghai free trade zone da wasu muhimman wuraren kasuwanci na kasar China domin ganin yadda za’a iya kawo irin wadannan cigaban a kasar Najeriya.

Ana tsammanin dawowar shugaban Kasa Buhari a mako mai zuwa bayan an cinmma yarjejeniyoyin da kasat ta China.

Idan za’a iya tunawa, Gwamna Fayose yayi Allah wadaran tafiye tafiyen da shugaban kasa Muhammadu Buhari keyi a kasashen waje. Ya bayyana cewa shugaban kasa yana kashe makudan kudade wajen tafiye tafiyen nasa wadanda hakan ke karya tattalin arzikin Najeriya.

The post Shugaba Buhari zaya ziyarci kasar China appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


Shugaba Buhari zaya ziyarci kasar China Reviewed by Olusola Bodunde on 09:08 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.