Sports Betting

Trending

random

Sojojin Najeriya sun gano rumbun abinci na Boko Haram

– Sojojin Najeriya sun samu babbar nasara akan kungiyar Boko Haram

– Sun gano rumbun da suke boye abinci

– Sun amshe wasu makamai dake hannunsu

Boko Haram

Bayan da suka samu gagarumar nasara akan yan kungiyar Boko Haram, sojojin Najeriya sunyi nasarar gano wani rumbu wanda yan kungiyar ta Boko Haram suke boye abincin su.

KU KARANTA: 

A wata takardar manema labarai da kanar Kakasheka Usman ya fitar, mukkadashin Daraktan labaran na sojin kasa ya bayyana cewa sojoji sunyi nasarar wargaza yan Boko Haram a Biggoro, Warpapa da Aura dake a kudancin Kumshe a karamar hukumar Bama. Sojojin Dibishan ta 7 ne kashi na 2 dana Task Force na 22 sukayi aikin.

Tace ” Dama amfani aikin shine domina kauda ragowar yan Boko Haram dake a wurin, suna ta tafiya suna dawowo saboda suna neman abinci da ruwan sha.

” Aikin yayi nasara domin sojoji sun gano duka wani wuri da yan Boko haram suke boye abinci kuma an lalata dukkanin su.

” Sojojin sunyi nasarar kashe yan Boko haram guda 2, sun amshe Bindigar Ak-47 guda 3, sun amshe mashina guda 3, kuma sun kwato yara  guda 2 dake hannun yan ta’addan.

Rahotanni sun fito a ranar asabar data wuce wanda suka bayyana cewa sojojin Najeriya sunyi musayar wuta da yan Boko Haram inda suka kashe yan ta’addan guda 30.

Birigediya Abubakar ya bayyana cewa hukumar soji bata bayyana inda matsugunnar ta yan Boko Haram take ba saboda wasu dalilai.

Ya bayyana cewa ana tsammanin yan kungiyar da yawa zasu aje makaman su a kwanakin nan saboda nasarar da ake samun a akan kungiyar.

 

The post Sojojin Najeriya sun gano rumbun abinci na Boko Haram appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


Sojojin Najeriya sun gano rumbun abinci na Boko Haram Reviewed by Olusola Bodunde on 05:45 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.