Sports Betting

Trending

random

Za’a kai yan bautar kasa sansanin yan gudun hijira

– Za’a tura masu yi man kasa hidima zuwa sansanin yan gudun hijira a Arewa maso Gabashin Najeriya

– Za’a kai likitoci da unguwannin zoma a wurin

– Mutane da yawa na a sansanin gudun hijira saboda Boko Haram

NYSC

Shugaban hukumar NYSC

Hukumar kula da masu yima kasa hidima (NYSC) ta bayyana cewa zata kai likitoci daga cikin masu yima kasa hidima sansanin yan gudun hijra domin su kula da su, cewar Birigediya Suleiman Kazaure.

Birigediya Kazaure ya bayyana hakan ne a Sansanin yan gudun hijira dake a Damare, jihar Yola, inda ya bayyana cewa manufar yin hakan shine don a sauwake masu wahalar da suke fama da ita.

KU KARANTA: 

Inda yake magantawa a Ofishin hukumar ta NYSC dake a Yola, shugaban hukumar ya bukaci ma’aikatan dasu kara zage damtse domin taimaka ma mutanen.

Kungiyar Boko Haram ta raba mutane Miliyoyi daga gidajen su.

Shugaban kuma ya bukaci masu yima kasa hidima din dasu taimaka ma yan sansanin gudun hijirar da aiyukan su na yau da gobe.

Shugaban kuma yayi kira ga mutanen Najeriya dasu hada kansu domin su ci galaba akan yan Boko Haram. Ya nemi kuma a yaba ma kokarin gwamnati.

Inda yake kaddamar da rarraba kayan masarufi ga yan gudun hijirar, shugaban hukumar ya yaba ma magabacin shi akan hangen nesa da yayi wajen fara hada shirin daya samar da sama da buhu 700 ga yan sansanin.

Mutane da yaw sun yaba ma masu yima kasa hidimar

Gwamnan Jihar Muhammad jibrilla ya sha alwashin tabbatar da cewa masu gudun hijira sun koma gidajen su zuwa karshen shekara.

Jibruila ya samu wakilci ne daga kwamishinan Noma, Amidu Waziri. Ya bayyana cewa zasu hada gwiwa da sauran Jihohin domin ganin haka.

 

The post Za’a kai yan bautar kasa sansanin yan gudun hijira appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


Za’a kai yan bautar kasa sansanin yan gudun hijira Reviewed by Olusola Bodunde on 02:53 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.