Kungiyar ‘Yan kwadago Zasu Matsama Gwamnonin Jahohi
Shugaban kungiyar yan kwadago na Najeriya ne ya bayyana hakan a Abuja a Ranar Alhamis 2 ga watan Yuni a wurin bude taron makillai na kungiyar ta TUC.
Shugaban ya nuna bacin ran shi wajen yadda gwamnonin suka karbo bashi $3.2billion daga bankin Duniya bayan kuma sun karbi bashi da babban bankin Najeriya CBN. Shugaban na TUC yace kungiyoyin su za su cigaba da yaki domin kyautatuwar rayuwar mambobin su ba tare da tsoron kowa ba.
Sannan ya kara da cewa “duk da cewa dokar kasa ta nuna cewar a biya ma’aikatan albashin shu a kan kari amma sai gashi wasu jahohin ma’aikatansu suna bin su bashi har na tsawon wata 9″. “A kun giyance kuma muna kira ga duk wani gwamnan da baya iya biyan albashi to ya gaggauta yin murabus daka mukamin sha.” Ya cigaba da cewa.
A wani labarin kuma mai kama da wannan Gwamnan Ekiti -Ayodele Fayose yayi kira ga ma’aikatan jihar tasa da suke yajin aiki da su janye kafin ya biyasu albashin na su.
Ma’aikatan dai sun shiga yajin aikin ne tun ranar Alhamis dan karshen watan jiya wanda kuma hakan ya sanya harkoki suka tsaya cik a jihar.
Gwamnan kuma ya bayyana cewar yanzu haka kudaden albashin ma’aikatan kananan hukumomi su nanan kuma za’a fara biya da zarar sun janye yajin aikin.
The post Kungiyar ‘Yan kwadago Zasu Matsama Gwamnonin Jahohi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us