Sports Betting

Trending

random

Rundunar Sojin sama ta ma ‘yan Boko Haram ruwan wuta

–      Rundunar Sojin saman Najeriya ta kai kai hari wata mazaunan yan ta’addan Boko Haram a arewacin Jihar Barno

–       Jami’an tsaron sun saki bidiyon samun nasarar tare da mika wata jawabi domin bayanin samun nasarar

–       Rundunar Sojin saman Najeriyan na cigaba da bada tabbacin ta na bada goyon bayan yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar bisa ga yunkurin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

 

An saki wata sabuwar bidiyo wacce ke nuna runduwar Sojin Najeriya masu suna ‘Operation Lafiya Dole’ ta kai ma yan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya,a ranar Alhamis.

sojin sama

sojin sama

Rundunar Sojin saman tayi amfani da jirgin yakin 2 xF-7Ni wurin samun babban nasarar a wani garin da ke tsakanin Tubun Rego da Malkonory, kimanin kilomita 25 daga garin Kangarwa a arewacin Jihar Barno. Bidiyon tazo ne kimanin awa 24 bayan kungiyar Boko Haram ta saki wani bidiyon nasarar da ta samu na kai hari gidan sojoji da ke Bosso,a jangoniyar Niger.

Kakakin rundunar ‘Operation Zaman Lafiya Dole, Ayodele Famuyiwa, yace a wata jawabi : “Mun ga wurin da suke daga na’urar kallon mu, suna amfani da na’urar sola domin samun sadarwa da wutan lantarki”.

“Mafi sabuwan harin da muka kai, Sojin sama ne suka kai harin a arewacin Jihar Barno domin karashe fitittikan sauran yan boko haram mai suna ‘Operation Gama Aiki’. Inda muka kai harin, mun dade muna lura dashi, wannan harin ya kawo ci baya sosai ga kungiyar yan Boko Haram,a yunkurin murkushe su gaba daya a yankin arewa maso gabas.”

KU KARANTA : Sojin Najeriya na cigaba da samun nasara akan Boko Haram

Bugu da kari, an kai harin ne ana cikin bikin Sallar azumi, wannan na nuna kokarin Rundunar sojin saman kasa na kawo karshen ta’addanci a yankin arewa maso gabas a cikin kankanin lokaci.”

The post Rundunar Sojin sama ta ma ‘yan Boko Haram ruwan wuta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.


Rundunar Sojin sama ta ma ‘yan Boko Haram ruwan wuta Reviewed by Olusola Bodunde on 04:14 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.